Daga: Bello Hamisu Ida
Fyaɗe wani mumunan al’amari ne da ya addabi al’ummar duniya,
inda wasu masu raunin zuciya da mugunta da kuma aniyar ƙuntatawa wasu suke
tursasa yara ƙanana ko matsakaita wasu lokutan har da manya ko tsoffi su aikata
masha’a da su.
An samu yawaitar aikata fyaɗe a ɓangarori daban-daban na
duniya, haɗa da Arewacin Najeriya, ko a watan da ya gabata an kama wani matashi
da ya yi wa wata tsohuwa fyaɗe, inda ya tsallaka cikin gidanta sannan ya
tursasata a Arewacin Najeriya.
Haka kuma, an samu gawar wata yarinya da aka yiwa fyaɗe bayan
an sace ta sannan aka jefa gawarta a cikin rijiya duk kuma a Arewacin Najeriya.
Akwai wasu Jihohi da suke gaggawar yanke hukunci ga wanda ya aikata fyaɗe, wasu kuma
Jihohin suna yanke hukunci ne ga duk wanda ya aikata fyaɗe bayan an ɗauki lokaci, wannan ya danganta ne da tsawon lokacin da shari'ar ta ɗauka da kuma tantance shaidun da aka samu.
Idan aka ziyarci gidajen yari, a kan haɗu da fursunoni wasu
matasa ko masu matsakaicin shekaru wasu kuma dattawa ko tsoffi waɗanda aka
yanke wa hukunci saboda an kama su da laifin fyaɗe.
Saidai kuna wani abun takaici, duk sanda aka kama wanda ya yi fyaɗe wasu lokutan a kan
lulluɓe zancen ne ko iyalai su ɓoye don tsoron kar sunan zuri’ar ya
ɓaci, ko kuma don kar a ƙi samun wanda zai auri yarinyar da al’amarin ya faɗa mawa.
Wannan rufa-rufar da ake yi yana ƙara taimawa sosai wajen yawaitar aikata fyaɗe.
A cikin Sabuwar Unguwa dake Katsina, an taɓa samun wani
mutumi da shekarunsa suka kai talatin da takwas zuwa arba’in, kullum ya kan ɗauki
ɗiyar makwabcinsa ya shiga gidansa da ita, yarinyar bata wuce shekara uku zuwa
huɗu ba. Wata rana sai aka kama mutumin ya yi wa yarinyar fyaɗe, bayan ya
tursasata sannan ya lalata mata gaba. An ɗauki yarinyar sumammiya sannan aka
nufi asibiti da ita. Da farko iyayen basu ɗauki wani kyakyawan mataki ba. Amma da
‘yan unguwa suka tabbatar da abinda ya faru, sai suka kira ‘yansanda inda aka
yi gaba da wanda ya aikata aika-aikar.
Wani ya shaida wa Arewa News cewa, a shekarun baya, lokacin
bai fahimci abinda ake nufi da fyaɗe ba, akwai wani ƙanin mahaifiyarsa dake
zaune a gidansu, akwai kuma wata ƙanwarsa da suka haɗa uba da ita, kullum
wannan ƙanin mahaifiyar sai ya ƙira yarinyar ya bata alewa sannan ya shiga ɗakinsa
da ita yana mata wasa, ashe aika-aikatar yake aikatawa da ita. Ranar da dubunsa
zata cika, sai aka kama shi dumu-dumu da ɗiyar yayarsa, amma wani abun mamaki
sai yayarsa ta ƙaryata abinda ake tuhumar ƙaninta da aikatawa. Hujarta kuwa ita
ce, wai ƙanin nata malami ne masanin hukunce-huncen addini. Wannan baluluɓa da
aka yi, ita ta ƙara taimakawa wannan ƙani nata, inda ya ƙara faɗaɗa ayyukan ta’addancinsa,
ya riƙa ɓata ƙananan yara tare da lulluɓe laifukansa da rigar addini.
Fyaɗe dai ya zama wani mumunan aika-aika da mutane basu tsoron
aikatawa saboda ruɗar sheɗan da biyewa dokin zuciya. Ta’asar aika-aikar ta saka
fargaba da tsoro da ɗari-ɗari ga al’umma, inda iyaye musamman masu rainon ‘ya’ya
mata suke tsoron miƙa ‘ya’yansu hannun wani.
Wasu lokutan ba makwabta ba ko ‘yan uwa na kusa har iyaye na
aikata fyaɗe da agololinsu koma ‘ya’yan da suka Haifa. Sau da yawa idan aka
kama wanda ya aikata a kan lulluɓe maganar a ji tsoron yaɗawa ga hukumomi, wasu
lokutan kuwa a kan fallasa wanda ya aikata laifin sannan a miƙa shi ga hukuma
don fuskantar hukunci.
Idan an ga masu aikata laifukkan fyaɗe ga ƙananan yara ko ma
manya da tsoffi ko maza a yi gaggawar sanar da hukuma ko wani na kusa da zai
taka muhimmiyar rawa. A guji aiken ‘ya’ya inda ba ada tabbaci, a guji sakin
yara suna yawo barkatai ba tare da bincikar inda suka je ko suke zuwa ba, a
guji sakin yara suna shiga gidaje da ɗakunan maza waɗanda ake da tabbacin basu
da aure, iyaye su bar barin ‘ya’yansu na yin wasa da wasu mazaje irin wasan da
ya wuce ƙa’ida, ko irin wasan miji da mata ko ma wasan zaulaya da taɓa inda bai
dace a taɓa ba a jikin yara musamman ɗiya mace, haka kuma da zaran an ga wani
abu da ake zargi, to a ɗauki mataki na gaggawa.
Wasu Labarai:
0 Comments