Daga: Hauwa'u Bello
KANO, NAJERIYA — Jiya ne aka wayi gari da wani abun Allah san barka, tare da taya Hafsat Idris murna da fatan alƙairi bisa auren da ta yi. Saidai an samu tangarɗa wajen yaɗa zancen mijin da ta aura inda wasu da dama suka yi da yaɗa cewa ta auri ɗan Sani Abacha, kodayake Mujallar Film ta tabbatar da cewa wata aminiyarta ce ta sanar da su cewa Hafsat ta auri ɗan gidana Abacha duk da yake bata ambaci asalin sunan wanda ta aura ba.
Saidai a jiya ne Mujallar
Film ta ƙara tabbatar da cewa ba ɗan Sani Abacha bane
angon Hafsat. Arewa News ta tattauna wa wani makusancin editan Mujallar mai
suna Hafiz Adam Koza, wanda editan ya tabbatar masa da ingancin rahoton da suka
sake samu na asalin wanda Hafsat ta Aura.
Haka kuma, Mujallar Film ta
ruwaito cewa, Muktar Hassan Hadi shi ne angon Hafsat Idris, kuma shi
ne wanda aka ɗaura mata aure da shi a asirce, ba ɗan
Sani Abacha ba kamar yadda aka wallafa daga farko.
Bayan bayyanar labarin ne, sai Hafsat ta kira wakilan Mujallar Film sannan ta jadadda masu cewa ba ɗan gidan Abacha ne ta aura ba, haka kuma ta sake wallafa wani saƙo a shafinta na Instagram inda ta ce,
“Assalamu Alaikum, Ina mika
sakon godiya ta ga dukkanin masoyana, ‘yan uwa da abokan arziƙi bisa
fatan alƙairi da suka yi mani, saidai ina so na yi magana a kan raɗe-raɗin
dake yawo musamman bloggers dake ta update a kai na cewa mijin da na aura na da
alaƙa da gidan Abacha, to wannan ba gaskiya ba ne, ba shida alaƙa da
su. Na gode.
“Babu
wani bayani da zan ba ku…”
Mahaifin angon, shi ma ya
tabbatar da cewa, ɗansa ne Hafsat ta aura. Daga bisani dai Mujallar Film ta sabunta
rubutun farko da ta yi sannan ta sace yin wani rahoto a kan sabon labarin da ta samu. (Arewa
News) www.arewanews.org.ng ko
www.arewa.com.ng
Bayan rashin Lafiyar Maryam Yahaya Sai Kuma Me Ya Faru Da Ita?
0 Comments