Daga: Bello Hamisu Ida
NASARAWA, NAJERIYA — Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yabawa Gwamna
Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bisa yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa a jihar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Mista Femi Adesina, a wata sanarwa da
ya fitar, ya ce Buhari ya yi wannan yabon ne a wajen wani liyafar cin abincin
dare a ranar Alhamis.
Shugaban wanda ya kai ziyarar aiki ta
kwanaki biyu a jihar, ya ƙaddamar da filin jirgin sama na Lafia, tashar
mota ta zamani, cibiyar koyar da sana’o’i, da hanyar Shinge-Barkini
Abdullahi-Kilema, wanda gwamnatin jihar ta aiwatar.
Ayyukan gwamnatin tarayya da shugaban ya ƙaddamar a ranar farko ta ziyarar sun haɗa da tashar samar da wutar lantarki mai
karfin 330kɓa da kuma ginin babban bankin Najeriya (CBN) dake Lafia.
Buhari ya bayyana jin daɗinsa kan yadda ake samun ci gaba a jihar da
kuma ingancin ayyukan da gwamnatin tarayya ta kaddamar a jihar.
Ya ce,
“Lokacin da na zo nan a ranar 6 ga
Fabrairu, 2019 zuwana na ƙarshe shi ne don neman goyon bayanku don ku zaɓe ni, tare da Engr. Abdullahi A. Sule a matsayin gwamnan
wannan jiha da sauran ‘yan
takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
“Dole ne in ce jihar Nasarawa ta ci gaba da
zama ɗakin gwaje-gwaje na
siyasa saboda ina bin hanyoyin ci gaba da gwamnatin APC ta yi, ta kuma samar da tsaro da ilimi, da ci gaban ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafawa matasa da mata.
Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta tabbatar
da kafa ƙarin rundunonin soji da
‘yan sanda a jihar da nufin samar da isasshen tsaro ga al’umma.
Ya lissafta su sun haɗa da Super Camps na Soja da ke Kenyehu da
Udege a ƙananan hukumomin Toto da
Nasarawa da runduna ta musamman guda 4 da ke ƙaramar hukumar Doma da Kwalejin horas da
‘yan sanda ta wayar salula da ke Ende-Hills a karamar Hukumar Nasarawa-Eggon da
Operation Whirl Stroke.
Buhari ya yabawa jami’an tsaro kan ayyukan
haɗin gwiwa da suka yi da
suka tarwatsa kungiyar ta Darul Salam da ke kewayen ƙaramar hukumar Toto da kuma shirye-shiryen
yaki da barazanar da suke fuskanta.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya ƙudirin gwamnatinsa na kara zage damtse
wajen tabbatar da rayuka da dukiyoyi.
“Ana tunkarar tashe-tashen hankula a yankin
Arewa-maso-Yamma da kuma wasu sassan Arewa ta tsakiya da ƙarfin tuwo. Za mu ci gaba da bayar da haɗin kai da jihohin da abin ya shafa domin
tunkarar kalubalen gaba daya,” in ji shi.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa
gwamnati baya, yana mai alƙawarin “ba za mu tsaya kan nasarorin da
muka samu ba, amma za mu ci gaba da ƙoƙarinmu na tabbatar da tsaro, da kuma ci
gaban Najeriya.”
A nasa jawabin, gwamnan ya taya shugaban ƙasar murna kan yadda ake tafiyar da
tattalin arzikin ƙasar, inda ya bada misali
da rahoton hukumar ƙididdiga ta kasa (NBS) na
baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa GDPn Najeriya ya ƙaru da kashi 3.98 cikin ɗari a rubu'i na hudu na shekarar 2021.
Gwamna Sule, wanda ya bayyana jihar a matsayin mai
zaman lafiya, ya gode wa shugaban ƙasa bisa gagarimar goyon bayan da ya bayar
wajen tabbatar da rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa bisa naɗa fitattun mutane na jihar a mukamai daban-daban a hukumomin
tarayya da suka haɗa da hukumar kula da
yawan jama’a ta ƙasa, hukumar kula da
lafiya matakin farko ta ƙasa, da kuma kwamitin bayar da lambar yabo
ta ƙasa.
Gwamnan, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kammala titin
Kwandare-Abuja, da asibitin koyarwa na Jami’ar Lafiya da kuma faɗaɗa layin dogo daga Abuja zuwa Keffi, wanda
ya haɗa da babban layin dogo a
tashar Guidi. (Arewa News) www.arewanews.org.ng
ko www.arewa.com.ng
Wasu Labarai
0 Comments