Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NAJERIYA - A wani saƙo da aka gani a shafin Tiwita na wata ‘yar jarida mai binciken ‘yar asalin Najeriya, Mrs Kemi Olunloyo, ta yi nuni da cewa wannan ɗan damfarar na intanet ɗa Najeriya wato Hushpuppi da aka yankewa hukuncin ya mutu a Amurka.
Jita-jita na nuni da cewa ɗa soshiyal midiya ɗin ya mutu ne yayin da yake hannun ‘yansanda a ƙasashen ƙetare.
Tun bayan kama Hushpuppi a ranar 25 ga Yuni, 2020 da Hukumar 'yan sanda ta Dubai ta yi, Kemi Olunloyo ke ba da bayanai game da kama shi da kuma shari'ar kotu wanda yawancin 'yan Najeriya da magoya bayansa ke bi a duk duniya.
Kodayake ba ta ambaci sunan Hushpuppi dalla-dalla ba, ta saba kiran Hushpuppi a matsayin 'Yaro'.
Tweet ɗin ya haifar da damuwa da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta tare, mutane da yawa suna ƙoƙarin samun ƙarin bayani ko fayyace yadda ya mutu.
Wani ya wallafa damuwarsa a shafinsa inda yake fata Allah yasa maganar mutuwar Hushpopi ta zama jita-jita ba gaskiya ba kamar yadda ake tsammani. (Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng
Wasu Labarai
0 Comments