Daga: Mujaheed Abdullahi Kudan
Shi lamarin fassara batu ne da yake buƙatar ƙwarewa da sanin makama kafin a yi shi. Da yawa masu fassara kalmomi kai-tsaye sukan fassara ne daidai da fahimtarsu, ba tare da wata madogara ba(a wani lokaci ma har 'yan jarida sukan yi wa fassara hawan ƙawara kuma al'umma su ɗauka. Daga nan kuma fassarar ta karɓu, duk da ba kan daidai take ba).
Kowane harshe da ya bunƙasa a duniya, yana samun cigaba ne ta hanyar karɓar baƙin kalmomi cikinsa sakamakon shigowar sababbin abubuwa daidai da sauyawar zamani.
Shi ya sa a lokacin da baƙuwar kalma ta shigo cikin kowane harshe ake ko dai fassara ta, ko a baddala ta daidai da ma'anarta ko siffa ko aikin abin da kalmar take yi a mu'amala ta yau da kullum. Alal misali, a da ana amfani da kura wajen ɗaukar kaya da sauran ayyukan da take iya yi. Amma daga lokacin da aka samu mota 'pick up' sai aka raɗa mata suna a-kori-kura (wato ta maye gurbin kura kuma ta ɗara kura biyan buƙata cikin sauƙi).
Amma kalmomi irin su 'fan', 'bucket' da sauransu ai baddala su aka yi kai-tsaye suka koma 'fanka', 'bokiti' daidai da tsarin sautin Hausa.
Saboda haka, kafin a kai ga riskar kalmar da ta dace da 'bestie' ko ƙirƙirar mata kini a Hausa, dole sai an dubi batutuwa kamar haka:
1. Daga wane harshe kalmar take?
2. Mene ne ma'anarta a harshen asali, idan kuma ba ta da ma'ana a wancan harshen to mene ne tushenta?
3. Mene ne ma'anar kalmar a Hausa, daidai da yadda ake amfani da ita tsakanin masu amfani da itan?
4. Duk wanda aka kira shi 'bestie' mene ne yake yi a tsakaninsa da 'bestie' ɗin nasa?
5. Shin muna da irin wannan mu'amalar a tsarin zamantakewarmu a ƙasar Hausa?
Waɗannan su ne za su zama madogara kafin a samu kalmar da za ta maye gurbin kalmar 'bestie' a Hausa, amma ba a fassara ta kai-tsaye da 'kwarto' ba.
Bari in ba da labarin wani tabbaci da nake da shi kan yadda na ci karo da kalmar 'bestie' lokacin ina saurayi.
Na taɓa yin wata budurwa wadda duk lokacin da na je zance wajen ta nake samun ta sanye da hijabi. Abin mamaki watarana na yi tafiya sai ta ce min in yo mata tsarabar gyale.
Ai kuwa haka aka yi. Na sayo mata gyale ɗan ƙasar waje. Sai dai na yi juyin duniyar nan ko sau ɗaya ta yafa idan na zo wajenta watarana in gani, ta ce sam ba ta san wannan ba!
Ana nan kwatsam watarana sai na ga ta sanya hotonta a Facebook sanye da gyalena ɗan ƙasar waje. Mutum na farko da ya fara yi mata 'comment' sai cewa ya yi; "bestie kin yi kyau", ita kuma ta amsa masa; "thank you bestie". Ni ma na zo da hanzari na ce mata; "Sweetheart kin kyau". Ina ta jiran 'reply' ta ce ba wannan maganar!
Ko da muka haɗu na nemi jin ba'asi sai ta nuna idan fa ina son zama lafiya in bar batun 'bestie' ɗin nan.
Bisa al'adata, ba na yanke hukunci ko in samu matsaya a kan kowane lamari sai na yi bincike. Saboda haka da na tsananta bincike da tattaunawa sai na tattara bayanan da na samu da kuma abin da ya faru da ni a wannan labarin sai na gane cewa:
1. Bestie ba saurayi(nki) ba ne, amma ya fi saurayi ƙarfin faɗa a ji wajen budurwa.
2. Saurayi shi ke lallaɓa budurwarsa, Amma bestie sai dai a lallaɓa shi.
3. Bestie ya fi samun dama a wajen bestie ɗinsa fiye da saurayinta(wannan zai iya haɗawa har da 'sauka shoulder'). Ƙila shi ya sa ake danganta shi da kwartanci.
4. Saurayi ke yin hidima ta kuɗi, 'bestie' sai dai a yi masa. A wani lokacin ma za a iya amsa a hannun saurayi a ba 'bestie'.
5. 'Bestie' yakan kasance babban mashawarci a wajen budurwa('bestie' ɗinsa), a wasu lokutan shi ne mai yanke hukunci a kan wane ne 'bestie' ɗin tasa za ta aura a cikin samarinta.
6. Kai-tsaye budurwa za ta iya nuna wa saurayinta 'bestie' har ma ta haɗa su abota, ko kuma saurayin ya nemi abota da 'bestie' ɗin budurwarsa saboda gyaran hanya, idan buƙatar hakan ta taso.
7. Budurwa/'bestie' ba ta ja wa bestie aji. Haka kuma 'bestie' ya fi kusanci da budurwa('bestie' dinsa) fiye da saurayinta.
8. A wasu lokutan daga 'bestie' akan rikiɗe a koma soyayya har a yi aure.
9. Wani lokacin ana cigaba da alaƙar 'bestie' tsakanin mace da namiji har bayan aure, idan mijin ya amince ko idan an fi ƙarfinsa, ko kuma a ɓoye.
10. A wani lokacin akan samu mace tana da 'bestie' ɗaya ƙwal babu saurayi ko kuma tana da samari da yawa. A wani lokacin kuma akan samu namiji yana da 'bestie' ɗaya ko fiye da haka.
11. A wani lokacin kamar yadda ake kishi a soyayya ta Allah da Annabi, haka ake yin kishi a mu'amalar 'bestie', musamman macen da ta ga 'bestie' ɗinta da wata macen, ko da kuwa ita wadda aka gani tare da shi ba 'bestie' ɗinsa ba ce.
Shi kuwa kwarto a ɗaya ɓangaren, namiji ne wanda yake mu'amala ta saduwa tsakaninsa da matar da ba tasa ba. Galibi gidan mijinta yake bin ta, ko ta biyo shi inda yake, ko su yi mahaɗa a wani wajen. A lura ba koda yaushe ba ne ake iya ganin kwarto da kwartuwa a tare, ko da za a gan su, to za a gan su ne suna wata mu'amalar ta daban wadda al'umma ta yarda da ita. Daga ranar da asirinsu ya tonu kuma, to fa abin kunya da abin ƙyama da yamaɗiɗi ya same su har da zuri'arsu.
Daga bayanan da suka gabata, bambanci guda ɗaya ya fito ƙarara tsakanin 'kwarto' da 'bestie' shi ne, kwarto a ɓoye yake kwartncinsa da kwartuwa 'yar'uwarsa, kuma suna kaffa-kaffa kada a san suna tare. Shi kuwa bestie a bayyane yake tasa mu'amalar da bestie ɗinsa, kuma ba da ƙyamar a san suna tare ba.
Ke nan, fassara kalmar 'bestie' kai-tsaye a matsayin 'kwarto' ba daidai ba ne.
Daga kalmar 'best' aka samo 'bestie'. Ita kuwa kalmar 'best' tana nufin 'mafifici'. Ta haka aka samu 'best friend' wato mafifici a cikin abokai. Wannan ta yi daidai da 'amini' a Hausa. Ita kuwa kalmar 'bestie' abin da take nufi a Ingilishi 'a person's best friend'. Ke nan, idan muka ɗauki wannan fassarar za mu ce 'bestie' ta fi dacewa a fassara ta da 'amini.
Sai dai inda gizon yake saƙa shi ne, shin al'ada ta yarda a yi 'amini' tsakanin mace da namiji? Domin ita dai kalmar 'bestie' kamar yadda ake amfani da ita a yanzu ta fi shahara a tsakanin samari da 'yammata. Amma a al'adance kuwa, namiji yana yin 'amini' ne da namiji ɗan'uwnsa, mace kuma tana yin 'aminiya' da mace 'yar'uwarta.
Wasu Rahotanni
3 Comments
Allah ya kara basira,bayanin ya fayyace komai sosai.
ReplyDeleteAssalamu alaikum!
ReplyDeleteAllah ya kara basira malan.
Tirka-tirka ke nan! Wato dai ƙawance da abota tsakanin mace da namiji shi ne ya sauya suna zuwa 'besty'🤔🤔
ReplyDeleteMun fa'idantu da wannan, Allah Ya ƙara fatahi.