Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NAJERIYA - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne wanda ke jagorantar babban taro dake
gudana na wasu manyan ‘yan siyasar Najeriya a ƙarƙashin wani yunƙuri da ka yiwa
taken The National Movement wato TNM.
Wasu sanannun mutane ne ke gabatar da taron cikinsu akwai Alhaji Tanko
Yakasai da Rufa’I Alkali da Buba Galadima da Aminu Ibrahim Ringim da Idris Wada
da tsohon Gwamnan garuruwan Jigawa da Kogi.
A wajen taron Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dake Jam’iyyar PDP ya ce, wasu ‘yan
Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje suka ƙirƙiri wannan
tafiya tasu mai albarka, ya ƙara da cewa, su waɗannan mutane ‘yan Najeriya sun
damu sosai da ci gaban ƙasarsu, sun kuma damu sosai da abinda ke faruwa a cikin
ƙasar, wannan ne yasa suka haɗu don su ceto ƙasarsu daga mawuyacin halin da ta
shiga.
Ƙungiyar za ta duƙufa sosai wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa da
ingata rayuwa da samar da abubuwan more rayuwa da kuma kawo ci gaba a cikin
birni da karkara.
Sanata ya ce, sun shirya tsaf don tunkarar matsalra tsaro da ta addabi
Najeriya.
Wasu Labarai
0 Comments