Talla

Ranar Rediyo Ta Duniya

 Daga: Bello Hamisu Ida

Ko kana sauraron Rediyo ko gidan ku akwai rediyo da ake sauraro kullum, Eace tasha ku ka fi sauraro a gidanku?

Wannan da ma wasu tambayoyin ne ya kamata a riƙa yi wa matasan wannan ƙarni ƴan bana bakwai. 

Ranar Rediyo ta duniya rana ce da hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe don tunawa da tasirin da kafar rediyo ke yi wajen sauya rayuwar al'umma, da kuma irin rawar da take takawa wajen bayar da bayanan abubuwan da ke faruwa a fadin duniya baki ɗaya.

A wasu ƙasashe kamar Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi, rediyo na matuƙar taka muhimmiyar rayuwa wajen kawo sauye-sauye a waɗannab ƙasashe, rediyo na ƙara samun masu amfani da ita inda suke sauraron ci gaba da ake samu a faɗin duniya, yanzu rediyo ta zama kafa mai muhimmanci a faɗin duniya.

Rediyo na matukar taimakawa kwarai da gaske musamma idan aka yi la'akari da irin shirye-shiryen da ake yi a gidajen rediyon.

A cikin duniya akwai abubuwa da dama da rediyo ke koyarwa, gidan rediyo na wannan zamani sukan gabatar da shirye-shirye tun daga na kiwon lafiya da kimiyya da fasaha da ilimin zamani da karatuttukan addini da shirye-shiryen dake raya al'ada dama sauransu.

Wasu gidajen rediyo sukan ƙirƙiri shirye-shiryen ɗaliban firamare da na sakandare da na ma jami'a. Haka kuma sukan wayarwa al'umma ta fuskar siyasa da wayar da kai da ta ɓangaren lafiya.

Wasu gidajen rediyon su kan gayyato shahararru ta ɓangare don su wayar da kai su ilmantar su koyar sannan su saka wani kyakyawan tunani a zukatan al'umma.

Bisa ra'ayin wasu kan irin tasirin da rediyo ke yi a rayuwarsu sun tabbatar da cewa, ba ƙaramin tasiri rediyi ta ke yi ba a rayuwar al'umma, saboda ita ce wadda talaka ma zai iya mallaka sannan ba a saka mata wani kuɗi kamar wayar salula wadda idan kana son ka karanta labari sai ka sayi data.

Masu sauraron rediyon sun ce ko rigar fulani kaje rediyo za ka tarar, kuma tana taimakawa wajen haɗa kan al'umma sannan ita ba ta ƙarya, ba kamar kafar sada zumunta ba.

Wasu Labarai:

  1. Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Hanifa Ya Buƙaci Gwmnatin Kano Ta Ɗaukar Masu Lauya
  2. Ɓarayi Sun Sace Mutane A Gidan Basarake Dake Ambarura A Sokoto
  3. An Kama Mai Kaiwa Bello Turji Makamai

Post a Comment

0 Comments