An karanta wannan labari tare da yin bitarsa wajen Reading Session da Kungiyar Marubutan Jihar Katsina KMK ta gudanar a ranar 12 ga watan Febrairu, shekara ta 2022.
****
Yara biyu ne kwance a kan
cinyoyin dattijuwar, murmushi kawai take tana shafa kawunan jikokinta,
kunnuwanta na sauraren yarda suke zuba surutunsu na yara.
Babban ne ya tashi zaune,
"Kaka, kaka! Yau wace
tatsuniya za ki yi mana?"
Murmushi ta yi tana kallonsa,
dama daidai take da katse su da surutun da suke, don ta sanar dasu wani abu mai
amfani.
Har lokacin murmushi bai ɓace
ba a fuskarta.
"Yau ba tatsuniya zan maku
ba, labari ne zan baku"
Ƴar ƙaramar ma ta tashi zaune.
"Yawwa Kaka ina son
labari"
"To ku saurara, labari ne
zan baku a kan wani Gwarzo, duk da bai yi suna ba, amma an san shi sosai a kan
taimakon mutane duk kuwa da kasancewarsa nakassashe.
An haife shi da lafiyarsa, ya
kuma girma da lafiyarsa. Saidai ya kasance shi maraya ne, Allah ya yi wa
mahaifinsa rasuwa tun yana yaro, sai shi da mahaifiyarsu da ƙanwarsa kawai.
Tun da ya kai ƙarfi yake
tallafawa mahaifiyarsa wurin kula dasu ta hanyar abinci da sauran abubuwan rayuwa.
Yana fita da safe shagon koyon ɗinki, idan an gama a sallame shi, da yamma kuma
ya ari mashin ɗin abokinshi ya tafi achaɓa. Mutum ne shi da bai raina sana'a ko
mai kankarta ta ba, yana da qoqari sosai wurin neman abin rufin asiri.
Kwatsam rannan ya fita achaɓa
da yamma, tsautsayi ya gifta mashi ya yi karo da wata mota, take ya faɗi a
wurin mashin ɗin ya fado a kan ƙafafunsa, tun a nan ƙasusuwan suka karairaye,
haka aka kwashe shi zuwa asibiti.
A ɗan abinda suka tara shida
mahaifiyar shi a kai mashi magani, har ya ji sauƙi ya dawo gida, amma fa babu
ƙafafuwa.
Ya shiga ƙunci sosai ganin
yanda abinda za su ci yake neman ya gagare su, gani yake nauyin gaba ɓaya
mahaifiyarsa da ƙanwarsa a kansa yake, amma ta ya ya zai taimaka masu bayan
wannan nakasa data same shi? Gashi duk wata sana'a da ya iya ta masu ƙafafu ce.
Mutane da yawa suna bawa
Mahaifiyarsa shawara a kan ta bar shi ya riqa fita bara, saboda naƙasar da yake
da ita mutane za su ji tausayinsa su taimaka ma shi da sadaqa.
Ta kan yi murmushi kawai ta ce
masu,
"Bakin da Allah ya tsaga
ai baya hana shi abinci, duk da halin da muke ciki, bamu rasa abin sakawa a
baki ba. Sannan ɓa na da kuke gani jarumi ne, duk da nakasar da yake da ita,
Allah bai yi shi cikin ƙasƙantattu ba, ni bazan ƙasƙantar da yaro na ya fita
yana roƙo mana abinda zamu ci ba, bazan sa wa yarona mutuwar zuciya ba, ina ji
a jikina zai samarwa kan hi mafitar da zai taimake mu, da sauran mutane insha
Allah".
Wannan yarda da mahaifiyarsa
tayi akansa, shi yake ƙara mishi ƙwarin gwiwa. Duk da haka ya rasa wacce sana'a
zai yi? Ta ya ya zai taimakawa mahaifiyarsa bayan ko shi baya iya yiwa kan shi
komai sai daga zaune? Baya iya fita koda harabar gidan sai da taimakon
mahaifiyarsu, yana ji yana gani ƙanwarsa ke fita ta yi talla, duk da baya so, amma
ba shi da wani dalilin da zai hanata.
Wata rana Abokinsa da suke
zuwa ɗinki a tare ya kawo masa ziyara, cikin firarsu dashi yake faɗa ma shi
yanda mutane da yawa sukayi kewar ɗinkinsa, saboda yanda yake yinsa da kyau
kuma babu ha'inci, da kuma yanda yake cika alƙawari yana yi a kan lokaci.
Maganganun da Abokinsa ya faɗa
masa suka sakashi ƙara zurfafa tunani, don haka mahaifiyarsa na zuwa kawo mishi
abincin dare ya tare ta da maganar da shi kanshi bai tunanin yiwuwarta.
"Umma ina so inci gaba da
ɗinki"
"ɗinki kuma?"
Ta tambayeshi cikin mamaki,
"Haba 'dannan, ta yaya
zaka iya ɓinki?"
Ta k'arasa maganar tana kallon
ƙafafuwansa, fuskarta cike da tausayin yaron nata.
"Dama nasan zakimun
tambayarnan Umma, zaki ce ta yaya zanyi ɗinki bayan bana da kafafuwan dazan
taka keke? Sai yanzu dubarar sakawa kan keken hannu yazo mun, idan aka saka
hannun daga zaune zan iyayi ba sai na taka ba"
Ta dan dauki lokaci shiru tana
tunani, sannan tace,
"tabbas hakane, na taɓa
ganin irin keken kuwa, insha Allah zaka ci gaba da ɗinki, basirar da Allah ya
baka na iya ɗinki bazata tafi a hakanan ba"
"amma Umma a ina zamu
samu keken ɗinkin? Wancan kudin dana tara na siyen keke har dasu aka hada wurin
biyan kudin Asibiti"
"karka damu, Allah bazai
hana yanda zamuyi ba, kaga tunda kan keken nema kawai baza'a kashe kudi da yawa
ba".
Gyaɓa kai yayi yana k'ara
tausayawa mahaifiyar tasa, tare da Addu'ar Allah yasa dinkin ya zamo musu
sanadin warwara.
Cikin satin kuwa mahaifiyarsa
ta samu rancen kuɗin da ta siya mishi keken na hannu mai sauƙin kuɗi, aka haɗa
mishi.
Mahaifiyarsa da kanta take
nemo mishi masu kawo mishi ɗinki cikin unguwa, da yake daman kafin ya samu
nakasar yana musu mai kyau, kuma baya amsar kuɓi da yawa, ya fara cikin sa'a
kuwa, ganin yanda ɗinkin nasa yake da kyau aka ringa kawo mishi daga maƙwaftan
unguwanni, dama wadanda yake yima dinkuna a baya, a haka har wasu garuruwan
suke kawo mishi.
Cikin shekara ɗaya ya buɗe
shagonsa, ya zuba ma'aikata, wasu nakasassu irinsa harma da masu lafiya suna ci
a ƙarƙashin sa.
Sannan yana ƙoƙarin taimakawa
naƙasassu daidai irin sana'ar da suke iyawa.
A cikin nakasassun nema ya
duba macen daya aura, wacce gobara ta ɓatawa hannu ɗaya da ɓarin fuska har wasu
mutanen suke gudunta.
Ƴar ƙaramar yarinyar tayi
caraf tace,
"kamar irin fuskarki
kenan Kaka?"
Murmushi tayi ta lakaci
hancinta da hannunta mai lafiyar.
"to ai wannan gwarzon ba
kowa bane sai Kakanku Alhaji Bello, duk da kasancewar baya raye a duniyar, yana
raye a zuciyoyin mutanen daya taimaka ma wa"
Babban yaron yayi magana cikin
sanyin jiki,
"Kaka Ina so nima idan na
girma na kasance kamar Kaka, na ringa taimakawa nakasassu yanda zasu dogara da
kansu, su daina yin barace-baracen nan"
"Allah ya cika maka
burinka, zanji daɗin hakan sosai, saboda dalilin baku labarin kenan, kuyi koyi
da kyawawan halaye irin na Kakanku, ku kasance masu taimakon nakasassu da masu
lafiya"
Suka haɗa baki.
"Insha Allah Kaka"
0 Comments