Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NAJERIYA — Sama da yara
miliyan goma sha uku 13 ne basa zuwa makaranta a ƙasar Najeriya, yaran sun haɗa
da masu talla da masu yawo bisa titi da waɗanda
ke zaune gida ba kuma masu barace-barace. Majalisar ɗinkin duniya ce ta fitar
da jadawalin ƙasashen da yara basa zuwa makaranta inda Najeriya ta zama a sahun
farko kuma ƙasar ta tafi kowace ƙasa yawan yaran da basu zuwa makaranta.
Bayan fitar da rahoton daga
Majalisar Ɗinkin Duniya, tuni dai ƙasar ta fara binciken yawan yaran da basu
zuwa makaranta. Ya zuwa yanzu an fara ƙidayar yara maras sa zuwa makaranta a
wasu jahohi dake cikin ƙasar.
Dr. Umar Buba Bindir ya bayyana
yadda shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa bayan ya samu rahoton MDD, ya ƙara da
cewa,
“Wannan dalili ne ya sa aka zauna
aka yi nazari sosai saboda muhimmancin da ilimi ke da shi a cikin al’umma”
Ya kuma ce,
“ba tare da bata lokaci ba
shugaba Buhari ya bayar da umurnin a ɗauki matakin da ya da ce wajen magance
wannan matsala, inda ya ce me zai hana a gina makarantu a kusa da inda yaran
suke, ta yadda ba za su rinka shan wahala ba wajen zuwa makaranta”
Ya kuma ce,
''Akwai
hukumar kididdiga ta ƙasa tana nan tana bin garuruwa da ƙauyuka don tantance
yaran da ba su zuwa makaranta”
Matsalar rashin
zuwa makaranta ga yara ba Arewacin Najeriya kaɗai ta yi ƙamari ba, babu inda ba
a samun yara maras sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar.
Ya kuma ce,
"Yanzu
mun shirya nan da wata ɗaya zuwa wata biyu za a fara koya wa irin waɗannan yara
abubuwa huɗu, wato turanci da lissafi da yadda za a zauna lafiya da kuma
sana'a".
Ya ƙara da
cewa,
''Sannan za mu rinƙa basu abinci sau uku kowa ce a rana,
akwai malamai da aka samar waɗanda za su koyar da yaran”
Bayan matsalar
rashin tsaro da tayi ƙamari a wasu jahohi dake ƙasar wanda ya taimaka sosai
wajen hana zuwa yara makaranta akwai kuma talauci wanda wasu iyayen suka ɗauka
cewa shi ne musababbin abinda ya hana su tura yaransu zuwa makaranta, kodayake
hukumomi da gwamnati na iyakacin ƙoƙarinta wajen kawo zaman lafiya da kuma
samar da ingantaccen ilimi a cikin ƙasar.
Wasu Labarai
0 Comments