Daga: Muhammad Abdallah
KANO,
NAJERIYA — Yau ce ranar litinin aka sake
yin zaman sauraron shari’ar mutumin da ake zargi da kashe Hanifa yarinya ‘yar
shekara biyar wanda wani malaminta mai suna Abdulmalik Tanko ya sace sannan ya
bata guba ta sha, daga bisani kuma ya binne ta tare da neman kuɗin fansa a
wajen iyayenta.
A ranar
7 ga wata ne dai mai shari’a ya ɗaga ƙarar zuwa yau, inda Abdulmalik ya nemi
gwamnati ta basu lauyoyi saboda babu wanda ke sauraronsu tun lokacin da aka
fara zarginsu da kashe Hanifa.
Bisa
zarge-zargen da aka karanto masu a gaban alƙali, Abdulmalik da Hashimu sun
musanta zargin sace Hanifa tare da yin garkuwa da ita haka kuma sun musanta
bata guba da kuma binne gawarta a ɗaya daga cikin harabar makarantar da shi Abdulmalik
yake yagoranta.
A wani
bidiyo da DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ɗora a shafinsa na fesbuk, an dai ga hoto
mai motsi inda aka ga Abdulmalik a cikin hoton, a cikin bidiyon, ya amsa laifin
da ya aikata sannan kuma ya nuna inda suka binne gawar Hanifa, haka kuma an ga
Hashimu wanda ya taimakawa Abdulmalik wajen binne gawar Hanifa, wanda shi da
kansa ma ne ya nuna inda ya rufe gawar sannan aka fiddo ta.
A wani
taron manema labarai, kuma Abdulmalik ya faɗi yadda ya kitsa sace Hanifa da
kuma yadda ya bata guba ta sha sannan ya binne ta.
Saidai
duk mutane ukun da ake zargi sun musunta zargin da ake yi masu, bayan an
karanto masu laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Fatima
wadda ita ce cikon mutum na uku da ake zargi, ta musanta zargin da ake yi mata
na haɗa baki wajen sace Hanifa, haka kuma ta musanta zargin da ake mata na
rubuta wasiƙa zuwa wajen iyayen Hanifa inda ta buƙaci a bada kuɗin fansa har
miliyan shidda.
Barista
M. L. Usman daga ƙungiyar Legal Aid da Barista P. A. Ademakun su ke kare
Abdulmalik da sauran mutum biyu da ake zargi da kashe Hanifa. Su ne kuma
lauyoyin da gwamnati ta bayar waɗanda za su kare Abdulmalik. Lauyoyin gwamnati
ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan sun nemi kotu ta ba
su damar kawo shaidunsu a zama na gaba.
Mai
Shari'a Sulaiman Naabba ya ɗage zaman kotun zuwa 2 da 3 ga watan Maris mai zuwa
don sauraron shaidu.
Bayan
kashe Hanifa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar Hanifa sannan
kuma ya jinjina wa 'yansandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa
Abubakar mai shekara biyar. Kisan Hanifa dai wani abun ban tsoro ne, wanda ya
tayar da hankullan iyaye tare da ɗalibai waɗanda ke zuwa makarantu don neman
ilimi.
Haka
kuma, Wani Mahaifi ya yi niyar ba mahaifan Hanifa ɗiyarsa mai suna Fatima don
rage masu raɗaɗi daga cin amanar da aka yi masu. Hanifa dai yarinya ce ƴar
shekara 5 wadda wani malaminta ya sace sannan ya yi mata kisan gilla ya kuma
binne ta a ɗaya daga cikin kangayen makarantarsu.
Malam
Abdullahi Ahmed Latus mazauni ne a ƙaramsr hukumar Darazo dake Jihar Bauchi ya
faɗi cewa tuni ya fara ƙudurta bayar da ɗiyarsa da mahaifan Hanifa domin rage
masu kewar rashin ɗiyarsu.
Saidai
kuma, Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona
makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan 'yar shekara biyar da ake zargin
mai makarantar da yi mata kisan gilla ta hanyar bata guba da cikin kwalbar lemu
ta sha sannan ya saka ta cikin buhu ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin harabar
makarantarsu, daga bisani kuma ya yi ta tsorata mahaifan Hanifa don su bashi kuɗin
fansarta.
Bayan
kashe Hanifa mutane sun ci gaba da yaɗa hotunan wasu yara da aka kashe bayan
kisan Hanifa, yarinyar da wani malaminta ya sace sannan ya kashe ta hanyar
sanya mata guba a cikin kwalbar lemu. An ta yaɗa hotunan wasu yaran da aka
kashe kafin a kashe Hanifa.
Satar
yara a garuwan Kano da Kaduna da Abuja da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya ya
zama ruwan dare, inda ake yaudarar yaran a sace wasu ayi masu fyaɗe sannan kuma
a nemi kuɗin fansa wasu kuwa kuɗin fansa ake nema sannan a kashe su. Ko
kwanakin baya saida aka kama wani mutum da yake cin naman mutane a garin Gusau
dake Jihar Zamfara wanda wani dake yi masa aiki ya sace wani yaro tare da kashe
shi. Ga dai jerin sunane wasu yara da aka sace waɗanda ake yaɗawa a dandalin
sada zumunta:
- Haidar Da Aka Sace A Unguwar Na'ibawa Dake Kano
- Aisha Sani Da Aka Sace A Tudun Wada Dake Kano
- Yaro da aka sace a Karkasara dake Kano
- An Sace Mohammed Kabiru Unguwar A Badarawa Dake Kaduna
- An Sace Husnah Garin Zariya
- Wata Uwa Da Ta Kashe Yayanta Guda Biyu A Unguwar Sagagi Dake Kano
0 Comments