Daga: Muhammad Abdallah
KANO, NAJERIYA - Abdulmalik Tanko shi ne malamin su Hanifa, kashe ta ne bayan ya sace ta sannan ya nemi kuɗin fansa a wajen mahaifanta.
A zaman da aka yi na shari'arsu a yau, ya buƙaci gwamnatin Kano ta basu lauya wanda zai kare su shi da sauran mutane biyu da ake zargi da kitsa sacewa da kashe Hanifa.
Wanda ake zargin ya faɗa wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta sama masa lauyan.
Abdulmalik ya ƙara da cewa,
"Ba mu da lauya a yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina roƙon gwamnati ta ba mu lauya,".
Sauran mutum biyu da ake zargi wato Fatima da Hashin Isiyaku, sun amince da abin da Abdulmalik ya faɗa na neman lauyan.
Lauyan gwamnati Musa Lawal ya yi ƙarin bayani inda ya ce, gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka buƙata.
Ya kuma ce, haka doka ta tanada saboda laifin da ake zarginsu Abdulmalik da aikatawa mai girma ne.
Mai Shari'a Sulaiman Na Abba ya ɗaga zaman shari'ar zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da ƙarfe 2:00 na rana.
Bayan kashe Hanifa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar Hanifa sannan kuma ya jinjina wa 'yansandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar. Kisan Hanifa dai wani abun ban tsoro ne, wanda ya tayar da hankullan iyaye tare da ɗalibai waɗanda ke zuwa makarantu don neman ilimi.
Haka kuma, Wani Mahaifi ya yi niyar ba mahaifan Hanifa ɗiyarsa mai suna Fatima don rage masu raɗaɗi daga cin amanar da aka yi masu. Hanifa dai yarinya ce ƴar shekara 5 wadda wani malaminta ya sace sannan ya yi mata kisan gilla ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin kangayen makarantarsu.
Malam Abdullahi Ahmed Latus mazauni ne a ƙaramsr hukumar Darazo dake Jihar Bauchi ya faɗi cewa tuni ya fara ƙudurta bayar da ɗiyarsa da mahaifan Hanifa domin rage masu kewar rashin ɗiyarsu.
Saidai kuma, Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan 'yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar da yi mata kisan gilla ta hanyar bata guba da cikin kwalbar lemu ta sha sannan ya saka ta cikin buhu ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin harabar makarantarsu, daga bisani kuma ya yi ta tsorata mahaifan Hanifa don su bashi kuɗin fansarta.
Bayan kashe Hanifa mutane sun ci gaba da yaɗa hotunan wasu yara da aka kashe bayan kisan Hanifa, yarinyar da wani malaminta ya sace sannan ya kashe ta hanyar sanya mata guba a cikin kwalbar lemu. An ta yaɗa hotunan wasu yaran da aka kashe kafin a kashe Hanifa.
Satar yara a garuwan Kano da Kaduna da Abuja da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare, inda ake yaudarar yaran a sace wasu ayi masu fyaɗe sannan kuma a nemi kuɗin fansa wasu kuwa kuɗin fansa ake nema sannan a kashe su. Ko kwanakin baya saida aka kama wani mutum da yake cin naman mutane a garin Gusau dake Jihar Zamfara wanda wani dake yi masa aiki ya sace wani yaro tare da kashe shi. Ga dai jerin sunane wasu yara da aka sace waɗanda ake yaɗawa a dandalin sada zumunta:
- Haidar Da Aka Sace A Unguwar Na'ibawa Dake Kano
- Aisha Sani Da Aka Sace A Tudun Wada Dake Kano
- Yaro da aka sace a Karkasara dake Kano
- An Sace Mohammed Kabiru Unguwar A Badarawa Dake Kaduna
- An Sace Husnah Garin Zariya
- Wata Uwa Da Ta Kashe Yayanta Guda Biyu A Unguwar Sagagi Dake Kano
Wasu Labarai:
0 Comments