Daga: Muhammad Abdallah
ZAMFARA, NAJERIYA — A wani gari dake cikin Jihar Zamfara, garin mai suna ‘yar Katsina al’ummar garni sun yi kira ga hukumomi da jami’an tsaro da su kai masu ɗauki saboda su samu kuɓuta daga hannun ɓarayin daji. Ɓarayin dajin dai sun sace yara da mata masu yawa, waɗanda aka sace ɗin sun kai kwana goma sha takwas a hannun ɓarayin.
Ɓarayin ɗai sun kai hari a garin ne ranar biyar ga
wannan wata inda suka sace mata da yara masu yawa waɗanda ake hasashen za su
kai ɗari ɗaya sannan suka shige daji da su, daga bisani dai sun sako tsiraru
daga cikin mutanen.
Rundunar ‘yansanda ta jihar Zamfara ta ce, bata da
tabbaci kan adanin mata da yara da aka sace a garin ‘yar Katsina, amma tana
iyakacin ƙoƙarinta don ganin ta kuɓutar da waɗanda aka sace daga hannun ɓarayin
daji.
Wasu Labarai
0 Comments