Daga Alƙalamin: Sister Iyami
‘Hi Baby, ya ki ke? fatan kin
tashi lafiya’.
Abin da na fara cin karo da shi kenan ta
akwatin sirrina na Fesbuk, bayan hawana online ƙarfe takwas na safe kamar yadda
na saba leƙa wannan sahar a duk lokacin da na wayi gari lafiya .
Na bi rubutun da kallo kamar me
son gane wani abu a cikinta, sai dai ban gane komai ba bayan ganin rubutun kamar na kullum daga abokan hulɗa dake
wannnan sahar, na yi banza da rubutun na ci gaba da duba manyan labarun da aka
tashi da su a wannann ranar.
Yamma lis, bayan na gama ayyukana
na yau da kullum, na ji ina buƙatar sake duba fesbuk don in ga me duniya ke
ciki.
‘Allah ya ƙara maki daraja, ya sa
ki fi haka 'yar uwa’.
Saƙon da na fara gani kenan ta
akwatin sirrina, na dai wannan sabon aboki nawa dana karɓe shi ƙasa da awa
ashirin da huɗu. Nazarin maganar nake ta yi tare da neman irin amsar da ta dace
in ba shi a wannann karo.
‘Ki aminta da ni 'yar uwa muyi
abota ta fisabillalahi’
Na ga ya sake turo mani wani saƙon,
saƙon da ya sake jefa zuciyata cikin tunanin abin da zance a karo na biyu.
‘Wataƙila kina tunanin abin da za
ki ce mani ko?’
Na tura sakon alamar dariya.
‘Duk yadda aka yi wani ya taɓa
wasa da zuciyarki a wannna sahar idan na ce haka ban yi kuskure ba’
Ya sake turo mani.
‘Ba haka bane’, Na samu karfin
gwuiwar rubuta masa.
’Amma kuma na ajiye magana tun
safe ba ki bani amsa ba?’
Dariya na yi da cewar, ‘ban gani
bane.’
‘Ke kanki kin san ba gaskiya ki ka
fada ba’
Wannan ne farkon alaƙata da sabon abokina da nake masa kallon mutum me
kamala da mutunci.
Na karɓi kyaututtuka masu tarin
yawa daga sabon abokina, kama daga kuɗi, sutura, waya zuwa katin waya, wanda
hakan yasa na ayyana shi a aboki na musamman, har daga baya ya bijiro da batun
son aurena. Ban ɓata lokaci ba na aminta da shi.
Bayan kwanaki ya zo mani da batun
uzuri ya kamashi ta tafiya ko zan rakashi? Na ji batun a sabon al’amari.
‘In raka ka zaka yi tafiya?’ Na
sake tambayarsa.
Ga mamakina sai na ga ya turon da
amsa cewa, ‘To meye a ciki?’
‘To a wani matsayi zan yi rakiyar
?’ Na tambaye shi.
‘A matsayin wacce zan aura’ Ya
bani amsa a takaice.
Ban bada amsa ba na sauka online
sai dai batun yayi ta mani kai kawo a cikin zuciyata.
Duk da ban yi rakiya ba wannann
karon tsarabar da na samu daga gareshi na dabam ne, ban yi farin ciki har can
ba saboda maganar rakiyar ta yi mani karan tsaye a raina. Haka muka ci gaba da
magana duk da ya fahimci na dan ja baya da shi tun a kan batun rakiyar.
Wannann karon da batun aurenmu ya
taso gadan gadan, na gabatar da shi ga iyayena kasancewar na taɓa aure. Sadaki
da kuɗin kaya haka ya bani a hannu, hakan ya rage mani kokonto a kansa. Ana sauran
sati ɗaya ɗaurin aurenmu, cikin dare sai ga kiran wayansa yana sanar da ni
tafiya ta taso masa washegari kuma yana so mu tafi tare. Kai tsaye na ce, ‘to’
kawai sai ka turo a ɗaura aure da asuba sai mu wuce.
‘Kina da matsala wallahi’.
Ya ce mani da alama a hasale
yake. ‘Auren nan kam ai duk alamun yin sa na nuna to meye ki ke mani haka ne
wai? Inda bana son aurenki da bazan tsaya har war haka ina asarar kuɗina a kan ki
ba’.
Shiru na yi ina nazarin
maganganunsa.
‘In ma ba zamu tafi tare ba zaki
iya samuna a Diamond Guest Inn akwai abin da nake son mu tattauna’.
Tun daga nan na ankara da salon
yaudararsa.
‘Na fahimce ka in kana buƙatar
tattaunawa da ni yanzu mu yi ta a waya, in kuma ba haka ba ka turo a ɗaura
aure, ko kuma in ka dawo ka zo ko ka turo a karba maka kuɗaɗenka’.
Hattara da mugun Boss aminin
bestie.
Wasu Kirkirarrun Labarai:
- Yadda Mata Ke Tallata Tsiraicinsu A Manhajar TikTok da Instagram
- Haddara Da Bestie
- Wane Mataki Zaku Ɗauka Idan Ku Ka Kama Wanda Ya Yi Wa Ɗiyarku Fyaɗe?
0 Comments