Talla

Me Yasa Hafsat Idris Ta Ɓoye Aurenta?

Daga: Hauwa'u Bello


KANO, NAJERIYA - A Jiya ne aka ɗaukawa Jarumar Kannywood wato Hafsat Ahmad Idris aure da ɗan tsohon shugaban ƙasa General Sani Abacha.

Ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022 ta zama ranar farin ciki da amarya da angonta da kuma masoyansu na kusa da na nesa, inda aka kasance cikin farin ciki da annashuwa tare da yi wa ango da amarya fatan zaman lafiya.

An ji ta bakin mujalar Film cewa, wata aminiyar jarumar ce ta sanar da ɗaurin auren wanda aka yi shi a asirce, majiyar ita ce ta tabbatar da cewa an ɗaura auren ne da ɗaya daga cikin ƴaƴan tsohon shugaban ƙasar. 

Majiyar ta ƙara da cewa, “Ɗan Abacha wanda aka haifa a Fadar Shugaban Ƙasa ne ta aura".

Ba a gano wane ne daga cikin ‘ya’yan Abacha ba wanda ta aura saidai ana tsammanin cewa tsakanin Abdullahi da ƙanen sa Mustapha ne angon.

Mujallar Film ta ƙara da cewq, An ɗaura auren a asirce a Kano, irin yadda wasu ‘yan fim ɗin Hausa su ke yi. Hakan ya sa ba mu gano inda aka ɗaura auren ba da sadakin da aka biya da kuma waliyyan ango da amarya.

Majiyar Mujalar ta ce, an tsara cewa babu wata walimar auren da za a yi kuma amarya za ta tare ne ba tare da ɓata lokaci ba.

Saidai Mujallar Film ta yi alƙawarin ci gaba da bincike domin gano wasu bayanan game da ɗaurin auren.

Ita dai Hafsat Idris, bazawara ce kuma uwar ‘ya’ya shida – mata huɗu, maza biyu.

Idan kun tuna, a watan Maris na 2021 ta aurar da ɗiyar ta ta uku, wato Khadija Kabir, wadda kuma a kwanan baya ta haihu.

Ta na daga cikin kyawawan jarumai mata waɗanda aka san su da iya shiga da tsadaddun kayayyaki.

Mu na mata fatan Allah ya ba su zaman lafiya.

Post a Comment

0 Comments