Daga: Hauwa'u Bello
Wata ƙungiya da ta haɗa da ‘yanmata da zawarawa mai suna Bayo Belwa dake Jihar Adamawa a Arewacin Najeriya ta yi barazanar barin yin kayan ɗaki. Sun yi barazanar ne bayan Majalisar dake kula da harkokin addinin Musulunci ta rage yawan lefen da maza za suyi.
Shugabar
ƙungiyar mai suna Fatima Ahmad ta shaida cewa, sun kira taro na musamman a ƙarshen
wannan mao don jin ra’ayin mata kan hukuncin da Majalisar Harkokin Adinin
Musulumci ta yi.
Shugabar
ta ce,
"An
sosa mana inda ya ke yi mana ƙaiƙayi, mun amince da dokar da Majalisar ta kafa,
sai dai kuma mu ma ƙorafinmu shi ne, suna da tabbacin idan aka yi auren cikin
sauƙi za a riƙe matan da ake aura?”
Ta
ƙara da cewa,
“A
yanzu hakan ana fama da yawan mace-macen aure, sai ka ga an yi aure da sati ɗaya
ko wata ɗaya ko shekara ɗaya an saki mace ba tare da dalili mai karfi ba".
Shugabar
kungiyar ta ce sun cimma abubuwa da dama a taron da suka yi, ta ce
"Abu
na farko da muka cimma shi ne, mutane susan cewa ba gwanjon mata ake yi a Mayo
Belwa ".
Ta kuma ce,
“Mun fitar da batutuwa game da sadaki, idan namiji zai biya sadaki da sauƙi to zai yi wa mace kayan aure, bayan haka kuma daga randa aka yi aure ta koma gidan shi kayan sun zama nata".
Shugabar ƙungiyar ta yi barazanar cewa, idan har maza ba za su iya yin kayan ɗaki ba to su ba matan kuɗin da suka kai darajar naira dubu ɗari uku 300 ga bazawara sannan su bada dubu ɗari takwas 700 ga budurwa. Ta kuma ce, da zaran an basu waɗannan kuɗi to lallai sun haƙura da lefe.
Ta
kuma ce,idan namiji ya zo ya tambayi auren mace to a yi bincike game da lafiyarsa
da kuma asalinsa.
Shugabar
ta yi bayanin yadda suka kafa wannan ƙungiya ta su, suna kuma goyon bayan duk
wani abun da Majalisar zata zartar, amma sun roƙi cewa suma a kalli nasu buƙatocin.
Daga ƙarshe dai Majalisar Harkokin Addinin Musulumci ta zo wajen taro ta kuma
ji duk abinda aka tattauna.
Wasu Labarai
0 Comments