Talla

Labarin: Ba Zan Ƙara Ba Na Ayuba Diskudo

Daga: Ayuba Diskudo

08032334446

Saɗaf-saɗaf, na ji an tunkaro ofishina, bayan yan daƙiƙu na ji an ƙwanƙwasa a hankali.. sai nace, yes, come in. Doguwa, baƙa amma kyakkyawar ɗalibata ce mai suna Mufida na gani riƙe da ƙofar kamar tana shirin komawa waje. Ta same ni ina shan lemun kwali wataƙila wannan ne dalilin. Na ce mata shigo mana. Anan ne to na ji tace, "afwan malam, Assalamu alaikum" zazzaƙar muryarta ta daki dodon kunnena. Na amsa mata, na kuma ce mata, ehe, what's the problem? 

Bayan na basar na fuskance ta. Cikin sanyin jiki da alamun jin kunya, tace; "sir, I want you to borrow me that book of yours" tana magana kan ta a sadde ƙasa, sai dai idanun ta kan tabkeken littafin Chemistry ne, *The Modern Organic Chemistry* da Albert Murphy ya rubuta. Haba Mufida na fa gaya muku bana bada aron littafi, na dai haɗa muku handout ga mai so zan bada copy a je ayi photocopy kyauta. Na jawo drawer teburi na na ɗauko copy biyu na bata, ta sa hannu biyu har da ɗan russunawa ta karba. 

Na ƙara ce mata ɗaya naki ne, ɗaya kuma ki ba captain naku ya faɗa wa yan aji duk mai so ya nema a wajen shi. Tayi godiya ta fice daga office. Bayan ficewarta ne na tsinci kaina cikin tunanin ta, na kuma rinƙa ganin surarta a ta giftawa ta gaban idanu na. Na tuno ranar da ta same mu a office ɗin HOD don ya saka mata hannu kan course registration form nata, bayan ta fice ne nacewa HOD wannan yarinyar akwai ƙoƙarin zuwa makaranta, sannan bata wasa a aji.. Anan ne HOD yace, "Mufida kenan, baiwar Allah. 

Shekara biyu kenan da rasuwar mijin ta amma ta kasa yin aure duk da manema da tayi da yawa". Na ce, yanzu wannan bata da aure? Sai yace, "ƙwarai kuwa, ka ga kullum tana cikin ƙaton hijabi ko? Ai haka tarbiyyar gidan su take. Baban su ba wani malamin addini bane, sanannen ɗan boko ne ma, amma tsari da tarbiyyar gidan sa na birge kowa". Allah sarki, ka ga abinda a yanzu yayi ƙaranci a zamanin mu. HOD yace, "ai lamura sun ɓaci sai addu'a kawai. Duk fa kasan babban abinda ya bata tarbiyyar yaran yanzu TV ne da uwa uba wayar salula".. Na ce gaskiya haka ne, Allah Ya rufa mana asiri kawai.

A karo na biyu, Mufida ta ƙara samu na a office wanshekare da na bata note kyauta. Yau ma kamar jiya ta shigo bayan ta ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Na ɗaga kai na kalleta a lokaci guda kuma na cire gilashin idanuna na ajiye kan tebur, na kuma dakata da danna malatsan computer ta na saurari abinda yau kuma me ya kawo ta. "Malam afwan na tsaida maka aiki, ina kwana". 

Lafiya lau, nace mata. Sai ta ce, "ga wannan kayan biki ne malam", ta zube wata farar laida maƙare da wani abu mai masƙi a ciki. "Don Allah ina neman afuwa gobe ina so a yafe min lacca bikin ƙanwata muke yi kuma nice babbar yayar su, akwai hidima da yawa, sir". To bikin da ba'a ma kai ga yi ba ni za'a kawo min kayan shi? 

Na tambaya. "Cincin ne da dubulan ai, an soya shi tuni shine na kawo maka" ta faɗa tare da yin murmushin da ya ƙara bayyana kyawun ta. Ba wani hoda ko janbaki ta sa ba, amma ta fito so fresh, murmushin ya bayyana dumful ɗin da ke kumatun ta duk da bakin ta bai bude a lokacin ba bare haƙora ta su bayyana. Nan take nace permission granted, hajiya Mufida. Da alamu ta ji daɗi sosai da faɗin hakan, tace "na gode, sir. Allah Ya ƙara ɗaukaka" nace aameeen. Amma ai baki gayyace mu ba. Sai tace, "You are invited, sir" a haka dai ta fice dauke da fara'a a fuskar ta.

Tayi ta zuwa wajena akai akai, har ta kai ga hatta matata ta san labarin ta. Ta ma je mata duniya asibiti a wani lokaci da aka mata CS a haihuwar ta da ta sami tagwaye. Haka mahaifiya ta ma ta san ta sosai. Ta taɓa ma zuwa har gida ɗauke da sabulla da turare ta ba Hajiyar mu. Da naji labari nace, kai Mufida, ya zaki taka har gidan mu haka ɗauke da kaya niƙi niƙi? Allah Ya saka da alkhairi amma please ya isa haka. Ni dai ban taɓa bata ko sisi ba, kuma ma kamar ko na bata ba zata karba ba. 

Kai abin dai ya fara ɗaure mini kai, kuma yana tsoratani. Matata kam tuni ta soma zargin muna soyayya ne da ita, kuma shirin auren ta kawai nake. Ta taɓa ce min, "hmmmn ayi dai mu gani, wai ni za'a yiwa wayo. Da kun ma fito fili". Ni dai ban ce uffan ba, don na san ko me nace ba zata amince ba. A ranar da na kwanta ma na jima barci bai dauke ni ba, nayi ta tunani kan lamarin har na tuno matsalar da na samu da matata sanadiyyar Asiya. Bari ku ji yanda ta faru tsakanina da ita;

"Ma'aruf kana da fara'a, ga abin dariya idan ka so, amma kana da saurin fushi". Asiya ce ta faɗa min haka bayan da na gama musu lacca na koma office ta bi ni can. Asiya ƙanwar aboki na ce kuma na lura ta saki jiki da ni sosai, sannan takan bani labarin yanda ɗalibai suke kallon ko wane malami. 

Hakan na birge ni don haka na ƙarfafa mata gwuiwa da ko meye kawai ta faɗa mini ba don komai ba sai don na san kurakurai na na gyara su. Yanzu dai ta faɗa haka ne akan dalilin da na disga wasu yan mata biyu a ajin sannan na kore su waje. Ban cika yin hakan ba amma ni kaina nasan yau a hasale na shiga makarantar sakamakon ɓatamin rai da wani mai mashin ɗin kabu-kabu yayi min a gidan mai. Da farko kaɗan na ce a kira min yan matan na basu haƙuri amma sai a ɗaya bangaren na ce a'a rabu da su ai laifi suka yi.

Ba wannan ne abinda nake son baku labari ba. Alaƙa ta da Asiya shine naso na zube muku da kuma yanda tayi tasiri wurin rabani da matata. Bana mantuwa da lokacin da Fahad aboki na ya zo da ƙanwar sa har makaranta don nema mata gurbin karatun NCE. Na ƙarfafa musu guiwar ta karanta Chemistry da Computer, da na san halin ta da ban yarda na zaba mata Chemistry ba tun da anan fannin nake koyarwa. Ina mugun son subject ɗin tun a Secondary hakan ya sa na karanta shi kuma nake son kowa ya zaɓe shi. 

Babban abinda ke birge ni yanda ake kuranta ni, har ɗalibai suka saka mini sunaye daban daban, kuma ban taɓa hana kowa kirana da su ba. Kaɗan daga ciki wasu na ce min; *Element*, wasu su kira ni da *Galileo*, *Bonding*, *Catalyst*, *Electrolyte* da sauran wasu duk sunaye na ne🤣. Asiya ta liƙe min sosai kuma ita ta gaya min ma ana kirana da wasu daga cikin sunayen.

Jabir abokina ne amma shi a fannin Computer ya ke, wata rana muna zaune da shi yake ce mini *Prof* kamar yanda wasu abokan aiki na suke kira na, na fa lura yarinyar nan kamar ƙaunar ka take. Na kalle shi nace mi yasa kace haka? Ƙanwar aboki na ce fa, so, a matsayin ya'ya kawai ta ɗauke ni. Jabir yace, "ka san so kamar programming ɗin computer yake, ko ina ce maka networking ma kawai. Ka san akwai wide area networking (WAN), to na gama karantar takun ta sarai, kawai son ka take". Da wannan misalin ni kuma tuni na shige fagena na Chemistry har ina can ina ta tuni a electrolysis yanda -ions da +ions suke bombarding suna migration to their opposites. Ka san "like charges repel, unlike charges attract each other". 

Wani lokaci daƙyar nake samun yin breakfast a gida, saboda haka ina shan yunwa a makarantar a farko. Amma daga baya sau ba adadi Asiya ta kan kawo kular abinci ta zauna ta zuba ta ce ta san yaya yana jin yunwa tun da ta ga nan na wuni. Daga gida take zuwa saboda bata kama daki a makaranta ba, wannan yasa ban damuwa sosai. Wani lokaci na ci ni kaɗai, wasu lokuta kuma na kira wani mu ci tare. 

Abincin karshe da ta kawo ta zuba ta bani, ta kuma dauko ruwan roba ta ɓalla marufi ta zuba a glass ta dalla min wani irin murmushi mai sanyaya gabobin jiki, sannan ta russuna ta miƙo min shi kan tebur tare da faɗin, "Ka san dambun couscous sai da ruwa kusa". Miyar sai mugun kamshi take, ga wata cinyar kasa a gefe. 

Na soma ci kenan sai kawai nace, ina son wannan irin abincin amma ka kai kayan miya a ɓata komai a kasa tsayawa a yi shi yayi daɗi. Har ga Allah ban yi nufin na faɗa a fili ba, ashe a bayyane na faɗi *shu'umar kuma ashe video take ɗauka ta* ban sani ba. 

A ranar ta turawa matata videon ta WhatsApp da wata number ba wadda na sani ba. Ina komawa gida nayi sallama aka ƙi amsawa, aka ƙi kula ni ma bare a wani kawo min abinci. Sai na ce, Sweety me ke damun ki ne? Ya na ga duk kin canza kuma lafiya na fita? Kawo min abinci to. Don na gane ta tsani ta dafa abinci na ƙi ci, don haka ko a ƙoshe na dawo sai na taɓa ko kaɗan ne. Auren soyayya muka yi, ya'yan mu uku. Bata taɓa yaji ba, ba wanda ya taɓa jin wani abu a tsakanin mu, ko mun bata da kan mu muke gyarawa.

Amma yau nayi duk dabarun da na saba yi ta ki sakin fuska. Na kunna TV, sai na ga akan tashar AfirkaTV3 take, wanda kuma kusan kullum na fi samun ta a Arewa24 kuma a kunne amma yau a kashe na same ta, ga baby na tayi tagumi fuska ba annuri. Na dauki remote na kama BBC World News don jin inda aka kwana akan tirka tirkar Russia da Ukraine. 

Ana ta nuno hotuna da yin bayani amma tsawon lokaci ban fahimci komai ba kamar bana jin turanci ko kaɗan. A cikin tunanin ne na jiyo muryar matata ba kamar yanda na santa ba, da alama ta ɗaga murya ne don tayi magana ban ji ba. Ji nayi ta ce, "tun da ban iya girki ba, jagula maka kayan miya kawai nake je ka kawo wadda ta iya ɗin ta rinƙa dafa maka, ina waigawa sai na gan ta cikin hijabi riƙe da jakar ta da niyyar ficewa daga falo.

Post a Comment

0 Comments