Daga: Bello Hamisu Ida
Labarin Da aka gabatar a taron bitar marubuta talatin da Pleasant Library Katsina haxin guiwa da Makarantar Malam Bambadiya ta shirya. Haka kuma an sake gabatar da tsakuren labarin a taron Reading Session da Qungiyar Marubutan Jihar Katsina KMK ta shirya.
An rubuta labarin musamman don yara su koyi ilimin Kimiyya da Fasaha da kirkire-kirkire kuma su san ma'adanai dake cikin kasar Najeriya.
***
Sannu a hankali
suka rikixe suka koma Maiki da Mikiya. Suka yi sama fir! Suka bar mai gona yana
mamakin irin hatsabibancin waxannan yara da suka yi masa varna.
Su ka yi ta
shawagi a cikin dajin Kamuku da ke qasar Zazzau wanda ya nausa ya haxe da dajin
Falgore na qasar Kano ya dangane da dajin Yankari na qasar Bauchi. Suna tafiya
suna kallon hotunan namun daji dangin su; zaki, kura, damisa, barewa, bacilmi,
ragon daji, raqumin daji, karkanda, macizai, yanyawa, giwar ruwa, qudan tsirya,
tsutsar katafila, tsutsar siliki da kwaron luna.
Maiki ya ce da
Mikiya,
“Shin kin
fahimci cewa, dabbobin sun kasu kashi biyu?”
Mikiya ta ce,
“Eh, na lura
wasu dabbobin na rayuwa cikin daji wasu kuma na rayuwa cikin ruwa, wasu jikinsu
rufe ya ke da kwasfa, ya yin da wasu jikinsu ke rufe da firkaki wasu kuma gashi
ya rufe jikinsu”
Sai Maiki ya
qara da cewa,
“Akwai dabbobi
masu qashin baya xaya kamar; maciji, kifi, qadangare da kada”
Bayan ya yi
shiru sai Mikiya ta ce,
“Haka kuma akwai
masu tafiya da qafafuwa huxu wasu kuma jan ciki suke yi, ya yin da wasu ke
tashi sama”.
Maiki ya ce,
“Ai in aka lura
ma cimakar dabbobin ta bambanta, barewa, giwa, veraye, fari, budari duk suna
cin tsirrai ne”
Sai Mikiya ta
ce,
“Amma zaki,
kura, damisa, maciji, kare, mangus, jemage, kwaxi da kifi duk suna cin nama ne,
waxannan dabbobi ai su ake kira da ‘maciya nama’”.
Mikiya ta xan yi
shiru sannan ta yi fir! Qasa, bayan ta nazarci tabbobin dake dajin Yankari sai
ta koma sama, sannan ta ce,
“Hallitar
dabbobin ma ta bambanta, qafafuwa da haqoransu an hallice su don su dace da
irin abinda suke ci. Haqoran kura dogaye ne masu kaifi za su iya yaga nama”
Ta haxiyi yawu
sannan ta ce,
“Haqoran Barewa
kuwa suna da faxi yadda za su iya tauna tsirrai su niqe su sosai”.
Daga nan Maiki da
Mikiya suka ci gaba da shawagi, sun haxu da dabar tsuntsaye da daular zuma da
fari, Maiki ya kama sarauniyar fara, fadawanta kuwa suka ce da wa aka haxa mu,
amma kafin su far masu da yaqi har sun sauka gefen kogi, suka sake yin siddabru
suka rikixa suka koma mutane.
Karambani ya yi
nitso cikin teku ya kamo sarauniyar kifaye. Suka haxa hallitun don su ga
bambancin yadda fara da kifi suke numfashi. Karambani ya xauko wani katako ya
xora sarauniyar kifaye sannan ya sanya itace cikin bakinta ya fiddo da
muqamuqin kifin, ya yanke su ya bar soson da ke ciki watau ‘gil’ mai ja-ja, ya
haska da tabaron hannu da ya xauko cikin jakar qudiri, ya ce,
“Sandunan dake
cikin (wato ‘gil’) mai ja-ja da sosansa masu alamar kaifi su ke motsawa ta
hanyar shaqar iska da fitar da shi, wato shi ne kamar huhun kifi, da shi yake numfashi”.
Karambana ya xauko sarauniyar fara ya haska
cikin bakinta da tabaron hannu sosai ya ga yadda take numfashi, ya ce,
“Ita fara bata
da muqamuqai kamar kifi (wato ‘gil’), bata da huhu, iska na shiga cikin wani
kwaroro ne zuwa cikin jikinta”
Ana kiran wannan
kwararo da Karambana ya gani a jikin fara da sunan‘sifarakul’ sun yi kama da
xigo-xigo da ke jikin fara. Daga nan sai suka yi zanen fara da kifi da abubuwan
da suka gani a jikin wata takarda sannan suka saka cikin jakar qudiri suka
nausa cikin daji suna bin gefen tekun don qara tantance abubuwan da ke rayuwa a
cikin daji.
Suna cikin
tafiya sai suka isa wani yanki. Yankin yana da arzikin duwatsu da ma’adanai,
masu cin wuta ta maras sa cin wuta kamar Kwal. Kwal wani ma’adani ne da ke
taruwa daga tsirrai. An fi samun sa a gabashin Najeriya. Shekaru aru-aru akwai
dogayen itatuwa a gefen wani teku da ke kusa da mashekari. Idan itatuwan suka
tsufa sosai sai su faxi cikin ruwa amma basu ruvewa, sai wata irin laka ta
lulluve itatuwa, a hankali sai itatuwan su narke su sauya kama su koma Kwal.
Wannan canji daga tsiro zuwa Kwal yakan xauki shekaru masu yawa. Wannan yanki
kuwa yanzu ya zama gari, sunansa Udi, yana can gabacin Najeriya kusa da Enugu.
Mafi yawancin ma’adanai
da ke cikin yankin Udi basa cin wuta, ruwa baya yi masu lahani, kamar farin
qarfe da jan qarfe, tagulla, azurfa ko zinari, dukkansu ruwa da wuta basa yi
masu komai. Saidai wasu daga cikin ma’adanai suna cin wuta, kamar kwal da
fetur, su waxannan an fi kira su da makamashi. Wasu sassan na qasa kamar garin
da su Karambana su ka baro watau ‘Yandaki, ana amfani da itace a kona don ayi
sanwa, amma wasu yankin suna amfani da kwal ko kananzir.
Karambani ya xauki wata
duga daga cikin jakar qudiri sannan ya haqo kwal, ya kale shi sannan ya ce,
“Akwai bambanci sosai
tsakanin wannan abu (kwal) da gawayi. Shi wannan (kwal) yana da nauyi da tauri”
Ya samo duwatsu sannan
ya kunna wa kwal xin wuta, ko bayan sun gama qona kwal xin ya kan yi ja-ja ya
koma wani launi bayan ya gama qonewa, savanin gawayi da yake komawa toka a duk
sanda aka qona shi qurmus, haka kuma kwal ya fi gawayi fitar da wuta mai zafi.
Abinda su Karambana da
Karambani ba su sani ba shi ne; duk lokacin da aka saka kwal cikin murhu, aka
kunna wuta, sannan aka hana iska yin shawagi a cikin wutar, kwal xin kan qone
sannan ya canza kala ya samar da wani sinadari wanda ake kira da qwan maqera
wanda maqera ke amfani da shi.
A wancan zamani
kuwa, turawa sun addabi yankin Udi, duk bayan lokaci sai wani bature ya je
garin sannan ya yaudare su su bashi ma’adanai ya tafi da su. Mazauna wannan gari
na Udi mutanen daji ne, ba sa son baqi; duk sanda baqo ya zo dajin sai su kama
don su shayar da abin bautarsu jini.
Suna ganin su
Karambana sai suka kama su, aka xaure su
tamau washe gari aka tasa qeyarsu ana kixa da rawa da waqoqi har zuwa wajen
bautar, aka sanya su cikin wani xaki aka rufe, aka kawo abinci da nama, da giya
da dukiya irinsu: kwal, tagulla, azurfa, zinari, farin dutse aka zuba cikin
xaki.
Da yake su ma
hatsabibai ne, ‘ya’yan Malam mai gani har bayan rai, kafin su fito yawon duniya
sai da malam ya shirya su sosai; sai suka yi lamo don ganin abinda zai faru.
Can da tsakar dare wani kabarin dake cikin xakin ya tsage wata irin hallita
fara sal! Mai kama da bil’adama ta fito, ta rarumi abinci ta ci, ta ci nama, ta
sha giyar da aka kawo sannan ta kwashe dukiyar ta koma cikin kabari. Kafin ta
koma cikin kabari sai Karambana ya yi wuf ya riqe qafafuwan wannan gawa, sannan
ya ce,
“Abin bauta muna
daga cikin dukiyar da aka kawo maka, amma ka zavi abubuwan da suka fi amfani ka
bar mu”
Hallitar ta yi
shiru, sai kuma ta fara qoqarin kwacewa don ta koma cikin kabari, amma suka
riqe ta tamau, da ta ji wahala sai ta fito sannan ta yi girgiza ta koma mutum
fari sal, ashe bature ne, yake yin shigar abin bautar su wanda ya daxe da
mutuwa. Da bature ya sha wahala sai ya nemi sasanci, suka sasanta sannan suka
shiga kabari tare. Cikin kabarin kuwa wata hanya ce da ta villa can cikin daji.
Daga nan bature ya yi siddabaru, ya hura hancinsa sannan wata ‘yar qaramar
tsuwa ta fito daga hancinsa sai wasu dawakai suka fito daga cikin jeji suna janye
da keken qarfe yayinda wani baqar tafa ke jan keken dawakan, baqar fatar yana
jin yarurruka fiye da goma cikin kuwa har da Hausa, shi ne ke fassara wa
baturen duk abinda aka faxa, duk da yake dai baturen yana ji. suka aza dukiya sannan suka hau suka nausa
suka nufi wani gari da ake kira Warri.
Warri wani gari ne da
yanzu yake a cikin Jihar Delta, ana kiran garin da ‘Birnin Mai’, garin yana da
arziqin ma’adanin mai da aka fi sani da fetur. Ana ce masa ‘birnin mai’ saboda
ya shahara sosai wajen haqo man fetur. Kamar kwal, Fetur ma wani ma’adani ne
wanda ake kira da xanyen mai. Ana samun man fetur a wurare da yawa a duniya,
kamar a cikin qasar Najeriya, ana samun xanyen mai a garuruwa: Delta, Rivers, Imo da Cross River. Ana samun mai a
qarqashin duwatsu da qarqashin qasa ko qarqashin teku.
Suna cikin tafiya sai
Karambana ya tambayi Bawa ya ce,
“Shin me yasa ka ke
biyayya ga turawa?”
Bawa ya kale shi sannan
ya ce,
“Saboda suna da abun
mamaki”
Karambani ya yi karab
ya ce,
“Shin sun fi jakar
qudiri abubuwan mamaki ne?”
Sai bawan ya ce,
“Bari mu isa ka ga
abubuwan mamaki da suke qerawa”
Suka xanyi shiru,
sannan bawa ya ce,
“Su ne suka fara haqo
Fetur”
Karambana ya ce,
“wace irin hallita ce
kuma fetur?”
Bawa ya ce,
“Babu wanda zai iya
cewa ga haqiqanin asalin fetur,an dai ce fetur ya samu ne sanadin wasu qwayoyin
hallita da ke rayuwa a cikin ruwa”
Ya xanyi shiru, bayan
sun haye wani kwazazzabo sai ya ci gaba da cewa,
“In waxannan halittu sun
mutu sai su nutse qasa, yashi ya lulluve su. Bayan tsawon lokacin waxannan
matattun halittu da ba su samun tattaciyar isa sai su canza su zama fetur”.
****
0 Comments