Daga: muhammad Abdallah
KANO, NAJERIYA - Hisbah a Kano ta kama mutum 78 maza da mata bisa zargin za su yi auren jinsi a wani gida da suka ɓoye kansu inda ake zargi nan ne suke aikata masha'arsu.
An kama su ne a wata Unguwar cikin Nasarawa GRA a wani gida da ake kira White House, inda aka ga mata da maza inda aka samu kwararon roba da ake amfani da shi don kariya daga ɗaukar ciki da kuma ɗaukar cututtuka daga abokin tarayya.
Yanzu haka mutanen da aka kama suna hannun hukumar Hisbah.
An yi zargin za su yi auren jinsi ko kuma suna halartar bikin, amma dai mutanen su musanta inda suka ce taron murnar ranar zagayowar haihuwar ɗaya daga cikinsu suke yi.
Yin auren jinsi a Arewacin wani baƙo al'amari ne musamman a Kano garin da ya zama cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.
Wasu Labarai
0 Comments