Talla

Hedikwatar Ma'aikatar Kuɗi ta Najeriya ta kama da wuta

 

Daga: Hauwa'u Bello


ABUJA, NAJERIYA - Hedikwatar Ma'aikatar kuɗi dake Abuja da aka fi sani da Ministery of Finance ta kama da wuta. 

Tuni ma'aikatar kashe gobara suka isa wajen sannan suka iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin sun kashe wutar. Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar.

Jaridar Punch dake Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce, ma'aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar.

A wani saƙo da ma'aikatar kuɗi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wani ajiyayyen batiri ne ya kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma'aikatar.

Wasu Labarai

  1. Abba Kyari Ya Musanta Zargin Da Ake Masa Na Safarar Miyagun Ƙwayoyi
  2. APC Ta Sake ɗage Babban Taronta Na ƙasa
  3. Mata Sun Yi Barazanar Barin Yin Kayan Ɗaki Saboda An Rage Yawan Lefe

Post a Comment

0 Comments