GABATARWA
DownloadAn rubuta wannan littafi mai suna ‘Hausa Firamare 3’ don ya yi daidai da manhajar koyarwar Firamare 3 (Primary Curriculum), zubin littafin ya yi daidai da sabuwar Manhajar Hausa wadda Hukumar Bincike da Habaka Ilimi ta Nijeriya (NERDC) ta sabunta a shekarar 2018. An sauya sunan littafin daga ‘Sabuwar Hanyar Koyon Karatu da Rubutu a Hausa’ zuwa ‘Hausa Firamare 3’ domin samu sauki wajen furucin sunan littafin.
Ga Darussan da ke cikin Littafi na Uku:
Jigo | Karamin jigo | Darussa |
HARSHE | A1. Sauraro Da Magana | A1.1 Ci Gaba Da Taɗi A1.2 Ƙarin Ƙidaya A1.3 Ci Gaba Da Sunaye A1.4 Ƙarin Kalmomin Aiki |
A2. Karatu | A2.1 Ƙarin Karatu | |
A3. Rubutu | A3.1 Ƙarin Rubutu A3.2 Tayar da Haruffa A3.3 Ƙarin Rubutun Gaɓoɓin Kalma | |
ADABI | B1. Wasan kwaikwayo | B1.1 Gajerun Wasannin Kwaikwayo |
B2. Waƙoƙi | B2.1 Ƙarin Waƙoƙin B2.2 Ƙarin Karin Magana Da Maganganun Azani B2.3 Gabatar Da Zaurane | |
B3. Zube | B3.1 Hikayoyi Da Tarihihi B3.2 Ƙarin Tatsuniya | |
AL’ADA | C1. Ɗabi’u Da Al’ada | C1.1 Kyawawan Ɗabi’u C1.2 Tsaftar Abinci C1.3 Ƙarin Wasannin Garganiya |
C2. Ginshiƙin Ginin Al’umma | | |
C3. Kayayyakin Al’adu | C3.1 Ƙarin Karikitan Cikin Gida |
A latsa nan Hausa Primary 3 don sauke PDF din littafin, Littafin kyauta ne ga Malaman Makaranta masu koyar da harshen Hausa Firamare 3. Idan an samu tangarda wajen saukewa a sake jarabawa.
0 Comments