GABATARWA
An rubuta wannan littafi mai suna ‘Hausa Firamare 1’ don ya yi daidai da manhajar koyarwar Firamare 1 (Primary Curriculum), zubin littafin ya yi daidai da sabuwar Manhajar Hausa wadda Hukumar Bincike da Haɓaka Ilimi ta Nijeriya (NERDC) ta sabunta a shekarar 2018. An sauya sunan littafin daga ‘Sabuwar Hanyar Koyon Karatu da Rubutu a Hausa’ zuwa ‘Hausa Firamare 1’ domin samu sauki wajen furucin sunan littafin.
Ga Darussan da ke cikin littafi na Ɗaya:
JIGO | KARAMIN JIGO | DARUSSA |
HARSHE | A1. Sauraro Da Magana | A1.1 Sunayen Abubuwa A1.2 Kalmomin Aiki A1.3 Taɗi A1.4 Ƙidaya |
A2. Karatu | A2.1 Karatu Kafin Fara Babbaƙu A2.2 Karatun Babbaƙu | |
A3. Rubutu | A3.1 Rubutu Kafin Fara Babbaƙu A3.2 Rubuta Babbaƙu | |
ADABI | B1. Wasan Kwaikwayo | |
B2. Waƙoƙi | B2.1 Waƙoƙin Yara B2.2 Waƙoƙin Baka Da Rubutattun Waƙoƙi | |
B3. Zube | B3.1 Tatsuniya | |
AL’ADA | C1. Ɗabi’u Da Al’ada | C1.1 Ladabi Da Biyayya C1.2 Gaisuwa C1.3 Tsafta C1.4 Ranakun Mako |
C2. Ginshiƙin Ginin Al’umma | C2.1 Kulawa Da Iyali | |
C3. Kayayyakin Al’adu | |
A latsa nan Hausa Primary 1 don sauke PDF ɗin littafin, Littafin kyauta ne ga Malaman Makaranta masu koyar da harshen Hausa Firamare 1. Idan an samu tangarda wajen saukewa a sake jarabawa.
0 Comments