Daga: Sister Iyami
Cikin zumuɗi da farin ciki na gama girke-girke da gyaran
wurin da zan yi wa abin ƙaunata masauki tsab. Jiran isowarsa kawai nake yi, ni
da kaina na gamsu cewar na yi kyau, bana buƙatar wani ya faɗa mani haka.
Kwatsam na tsinkayi wayata na ruri, cikin sauri na ɗauka duk
a tunanina masoyina ne, sai da na amsa na ji muryar BESTIE na. Cikin isa da
gadara ya ce mani,
“Ya iso ne ko har yanzu?”
Da sauri na ce,
“Yana hanya na sani, kila go-slow ya tsayar da shi”
Ya yi saurin katse ni ya ce,
“Kina da matsala wallahi, wannan gayen ya rainamu da yawa, saboda
haka ko ya zo ba zai samu ganinki ba shi ne gaskiyar magana, ya yiwa kansa ki
saurare ni ganinan zuwa”.
Cikin mintuna ƙalilan BESTIE ya ƙaraso gidanmu, kai tsaye ya
wuce inda na shiryawa masoyina babban baƙona gara a matsayinsa na wanda zai yi
zuwa na musamman a kan maganar aurenmu.
Ya fara kwasar garar da ba don shi nayi ba. Duk yadda nake
jin sa a cikin zuciyata yau dai bai kyauta mani ba, ana haka masoyina ya kira
wayata, BESTIE na shi ya amsa kiran ya ce cikin gadara,
“Ka na ji ko? yau dai ba zaka samu damar ganinta ba saboda ga
alama baka respecting time”.
Ya tambaye ta cikin wayar ya ce,
“Kai kuma wanene haka da zan kira ta ka ɗaga kana bani wannan
amsar?”
BESTIE cikin jin haushi ya kallleni tare da tambayarsa ya ce,
“Ashe bata baka labarina ba? kai tsaye ni ne BESTIE ta”
Ya faɗa ba tare da jiran jin amsar tambayarsa ba. Ya ƙara
cewa,
“Sai na aminta da kai zata saurare ka har ka samu damar
auranta. Don haka na gama magana yau dai ba zaka samu ganinta ba, ya katse kira”.
Hawayen takaici ya subuce zuwa kan fuskata, kasancewar girma
da darajar mutumin ya wuce ayi masa haka.
BESTIE ya kalleni wato
ke har kin fara son sa za kiyi kuka don an hana shi zuwa? Daraja da mutunci
nake son sa ma maki a wurin mutumin nan. Cike da baƙin ciki nake maganar,
“Wace irin daraja da mutunci kake nema mani saboda Allah ?
Duk mutanen baya da ka korar mani suma daraja da mutunci kake nema mani, shi ya
sa ka kore su ko ya ka ke nuif?”
Ya ce,
“Aw! ina ta ƙoƙari a kanki BESTIE ashe ke haushina ki ke ji har kin kullace ni da
korar masu son aurenki?”
Ya yi shiru sannan ta ce,
“Tsakani da Allah BESTIE wannan shi ne karo na biyar kana
mani haka k..”
Ya yi saurin katse ni da cewa,
“Ki zaɓa ko ni ko shi”.
Cikin kaushin murya na ce,
“Ka ƙaddara mun rabu har abada in har wannan mutumin ya janye
batun aurena, kuma Allah ya isa tsakanina da kai”.
BESTIE ME?
0 Comments