Talla

Har Shayin Ya ƙare?

Daga: Hafiz Adam Koza

Wani ango ne da amaryarshi suka hayyaci wani tsoho da ke maƙwabtaka da su a gidan haya; ga ɗaki ga ɗaki. Waɗannan sabbin ma'aurata kullum da dare sai su sanya waƙar nan ta,

''Fifita mini shayi, ka sanya mini Luna; madara!''

Wannan lamari na damun tsohon a kullum, har ba shi samun isasshen barci saboda ƙure balum da suke yi, ya dai ci gaba da haƙuri.

Watarana cikin dare sai ga amarya ta fito tsakar gida a guje, tana kuwwa da hurwar neman agaji. Tsoho ya fito daga ɗaki cikin sauri domin ya ga me yake faruwa. Yana fitowa suka yi kaciɓus da angon nan riƙe da bel a hannunsa, ya yi kan amarya yana huci a fusace. Tsoho na ganin haka sai ya ce da ango,

''Yaro kar dai in ce har shayin ya ƙare?''

©Hafiz Koza.

Post a Comment

0 Comments