An rubuta wannan littafi mai suna ‘Hausa Firamare 4’ don ya yi daidai da manhajar koyarwar Firamare 4 (Primary Curriculum), zubin littafin ya yi daidai da sabuwar Manhajar Hausa wadda Hukumar Bincike da Haɓaka Ilimi ta Nijeriya (NERDC) ta sabunta a shekarar 2018. An sauya sunan littafin daga ‘Sabuwar Hanyar Koyon Karatu da Rubutu a Hausa’ zuwa ‘Hausa Firamare 4’ domin samu sauki wajen furucin sunan littafin.
Ga Darussan da ke cikin Littafi na Huɗu:
Jigo | Karamin jigo | Darussa |
HARSHE | A1. Sauraro Da Magana | |
A2. Karatu | ||
A3. Rubutu | ||
ADABI | B1. Wasan Kwaikwayo | |
B2. Waƙoƙi | ||
B3. Zube | | |
AL’ADA | C1. Ɗabi’u Da Al’ada | |
C2. Ginshiƙin Ginin Al’umma | ||
C3. Kayayyakin Al’adu |
A latsa nan Hausa Primary 4 don sauke PDF ɗin littafin, Littafin kyauta ne ga Malaman Makaranta masu koyar da harshen Hausa Firamare 4. Idan an samu tangarda wajen saukewa a sake jarabawa.
0 Comments