Wannan taɓa ka lashen Kyauta ne. Amma ga mai son jin cikakken labarin littafin za a biya kuɗi kaɗan.
Gargadi:-
Yin Amfani da Basirar Wani Kai Tsaye Ba tare ds neman Izininsa ba Karya doka ne. Don haka ga mai son yin amfani da wani sashi ko kuma gaba dayan dukkan labarin zai iya tuntubar Marubucin. 080-65418892.
*****. *****. *****
2
Ledojin Da na ciko da Take away na Ƙoƙarin Suɓucewa su Tarwatse a ƙasa a hannuna saboda irin Kallon da Anti Yusrah ke min.
Nayi hanzarin Riƙo su gami da matsawa gaba kaɗan. Don Kar ta Kawo min Hannu.
Tsahon minti guda tana kallona cike da takaici. Sannan Tace.
"Sai ki ajiye ki ɗauko Plate ki juye. Mu ga abinda kika siyo. Kin san dai Oga ba Kowane abinci yake ci ba Saboda ciwonsa. Kuma kin san dalilin da yasa nace ki kawo min abinci daga gida saboda mara lafiyar ne".
Nayi hanzarin ajiye ledojin gami da matsawa gaba kaɗan wajen da Fridge yake da ƙaramar Loka inda suke tara kayan da suke amfani dasu.
Na kwaso Plates da Spoons na Kawo mata. Sannan nace ina zuwa zan duba wani abu a waje.
Ban jira ta bani amsa ba. Nayi hanzarin barin Ɗakin.
Na nufi Kafar Bene inda mukai taho mu gama da Wannan Mutumin da yayi min ɓarin kayan abinci.
A ƙasan benen anyi wajen Ma'aikata masu Goge-Goge da Shara. Nan na nufa. Nayi sa'a na tarar da wani Garjejen Mutum Baƙi. Bayan na washe masa baki na tambayeshi ina neman wasu kaya da na bari ne Ɗazu a Kafar Bene. Ko ya kula ya gansu. Ko kuma wani daga cikin ma'aikatansu sun gansu sun kawo don ayi cikiya?.
Kamar anyi masa Gafara. Ya Wangale wakeken bakinsa. Da rawar Jiki yace min ai yaga sanda na barsu na fita a guje. Don haka ya kwashe ya adana.
Ya cigaba da cewa.
"Amma ga dukkan alamu abincin ya tarwatse. Ya haɗe da Miyar da kuma Lemo da Fruit Salad ɗin da yake ciki".
Nace. "Ba matsala! Kayi amfani dasu. Anjima zanzo na Karɓi Kwanukan idan zan wuce gida Bayan Magriba".
Ya sake rusunawa yana godiya. A ransa ƙwarai ya ji daɗin abinda nayi masa. Sannan kuma ya dinga jin tamkar Yau yafi Kowa takar sa'a a yinin Yau gaba ɗaya saboda kyautar da akai masa na abincin duk da ya haɗe. Amma ya san zai mori zuƙu-zuƙun cinyoyin Kazar da ke cikin miyar.
***** ***** *****
Kafin magriba 'yan gidansu Yaya Taneem sun zo dubashi zuga guda( Ma'ana da Yawansu). Sannan a ɓangaren gidanmu. Mamanmu da yaran Anti Yusrah suma sun zo Duba shi.
Alhamdulillah! Jikinsa na samun sauƙi. Don haka ya samu ya farka daga barcin da yake yi. Kuma ya ɗan ci abinci yasha magani. Daga ɓangaren 'yan gidansu ma sun kawo masa himilin abinci da kayan dubiya. Don haka zauna anata hira kamar ma ba a asibiti muke ba.
Don haka na ƙara samun damar da zan koma na kewaye harabar Asibitin ko zan ga wannan mutumin da yayi min ɓari kuma ba tare da ya tsaya ya bani haƙuri ko ya tayani kwashewa ba.
Hankalina ya tashi da na tuna ba zan iya gane fuskarsa ba. Don taho mu gama muka yi kuma babu wanda ya zaci zai haɗu da wani. Ma'ana dai Kicibus muka yi. Kuma bai tsaya ba sanda muka hadun. Don haka ban ga fuskarsa ba. Shi ma kuma bai ga fuskata ba. Abinda zan iya ganewa dashi shine kawai na kula da bayansa. Sai ƙirarsa naga yana da Tsayi amma ba can ba. Sannan kuma Baƙi ne. Sai kuma ƙananan kayan da yake jikinsa wanda miyar da ya zubar min ma ta ɗan fallatsa a jikinsa.
Abu ne mai wahala ga mutumin da baka sani ba ka iya ganeshi don kawai ka ganshi ta baya. Wanda ka sanine sosai zaka iya shaidashi ta baya.
Don haka nace to ko haƙura zanyi da nemansa tunda Allah ya takaita min wahala bai ji min ciwo bama da muka yi kicibus ɗin.
Zuciyata tayi sanyi da na tuna na gane kalar motarsa. Kuma na riƙe lambar motarsa tabbas sanda nake binsa a baya a mota. Sannan kuma ai na bi shi naga har gidan da ya shiga duk da bani da tabbacin gidansu ne? ko gidansa ne? Ko kuwa wani gidan dabam
ya shiga?.
Karfe takwas na dare bayan munyi sallar Isha a Asibitin muka yiwa Anti Yusrah sallama da shi kansa Yaya Taneem ɗin tare da yi masa fatan Allah yasa gobe a Sallameshi don jiki ya fara kyau.
Yaranta suka ce ni zasu bi a motar da nazo da ita. Mamanmu tace a a su biyota ita da Driver tunda daman can shi ya kawo su.
Nayi dariya nace.
"Mama Ki barsu su biyoni zan tsaya a Silver Bird na siya musu Ice cream da Samosa ko Pizza wadda zasu tafi dashi School gobe kin ga ba sai an sha wahalar tashin sassafe yi musu girki ba".
Yara Kuwa suka hau tsalle suna faɗin.
"Yehh! Anti Nuzlah zamu biki Silver Bird. Ba zamu bi Mama Gida Yanzu ba".
Mama ta Gallamin Harara. Tace.
"Yar Nema daman abinda take so kenan ta haɗani da Jikokina. Sai ku Bita. Amma Kar ku wuce Karfe 9 kin san Alhaji(Wato Mahaifinmu). Baya Son Yawon nan fa na dare".
Ina Dariya nace.
"Insha Allah Mama ba zamu wuce 9 na daren ba. Abinda na faɗa miki shi kaɗai zamu siya sai chocolate da Biscuits mu juyo gida".
*****. ******. *****
A Silver Bird duk Namiji Baƙi mai ɗan Tsayi idan na Gani sai nayi ta kallonsa ina tunanin Ko shine mutumin nan na ɗazu da ya zubar min da kayan abinci. Har wasu Mazan ma suka dinga tsarguwa da irin kallon da nake yi musu.
Mazan da suka zo kuwa tare da Matansu. Idan matan suka kula da irin kallon da nake musu sai kaga Mace na wani murtuke fuska gami da kaffa-kaffa da Mijinta. Ita a Ranta tana zaton ko zanyi mata Kwace ne.
Mun ciko Ledoji Cike da Kayan Kwalam da Makwalashe ni da Yara. Muka wuce gida muna ta hirarmu amma ni kuma zuciyata cike da tunanin son ganin mutumin nan don naji dalilin da zai min barin abinci kuma yaki tsayawa ya bani Haƙuri.
A ɗaya ɓangaren kuma ina son sanin menene dalilin Saurin nasa haka, wanda har saurin yasa kamar ya fita daga hayyacinsa ma lokacin da yake saurin.
***
Mun baje wasu ledojin da muka siyo a Falo ni da Yara Sai Mama Da Abbanmu. Sauran Ledojin kuwa muka adanasu a Freezer.
Abba Ke tambayata Yace.
"Nuzlah wai yaushe za a saki Mobilization List ɗinku ne na tafiya Service (Ma'ana NYSC)?".
Kafin nayi Magana tuni har Mama ta rigani da Cewa.
"Nima dai naga wannan karon kamar an samu delay. Wajen wata Shida Yara na zaman Jira".
Abba Yace. "May be delay ɗin na da alaƙa da Wannan Rikicin Kabilancin gami da Ta'addancin 'Yan Bindiga da Masu Garkuwa da mutane, da ake fama dashi a wasu Yankunan Kasar nan. Shine ya janyo delay ɗin".
Bakina Cike da Lomar Casadelles Bugger nace.
'"Abba kuma kasan da yake wannan Gwamnatin ba kamar ta baya ba. Su komai nasu ana samun jan ƙafa shine yasa".
Mama ta gallamin harara tace.
"Sai ki bari ki gama haɗiye lomar da ke bakinki. Sannan kiyi magana kar ki je ki ƙware. Kin san dai ba kyau mutum na ciye-ciye kuma yana surutu ko?".
To haka dai muka kammala ciye-ciyenmu da yan kallace kallacenmu har muka tattara kowa ya nufi makwancinsa.
Ina shiga ɗaki bayan na watsa ruwa a jikina don naji daɗin barci. Na saka kayan barci. Dogon wando da riga na Transuit. Na saka Hula akaina duk da Gashina Ya fito ta gefe.
Na Baje a Gado. Yayin da na dauko Wayata daman Laptop ɗina na kan Gadon a jone jikin Caji.
Nayi niyyar kunna data na hau Social media naga wainar da ake toyawa a Facebook da Instagram. Yayin da kuma nake son na shiga WhatsApp na duba group ɗin mu na School naga ko akwai wani Update game da tafiyarmu NYSC.
Gabana ya yanke ya faɗi Ras! Saboda ganin wajen 17 Missed Called. A wayar kafin ma na buɗe datar. Don haka na haƙura da buɗe datar.
Nayi hanzarin dubawa naga ko suwaye suka kirani. Ashe na manta sanda zanyi sallar Magriba na saka wayar a Silent.
3 Missed Called na ƙawata Mahfuzah ne. 2 Missed Called na Nabeel Class mate ɗina ne. Sauran Missed Call 12 kuwa 3 baƙuwar lamba ce. Ragowar kira Taran kuwa na Sahibina Musayyib Bala ne.
Hannuna na rawa duk banbi ta kan kiran sauran ba. Nayi hanzarin danna lambar Rabin Raina Musayyib.
A zuciyata nace yau zan sha masifa da ƙorafinsa. Zan rasa ma hanyoyin da zanbi don bashi amsar kare kaina daga wannan jerin gwanon kiran da yayi min har guda Tara.
Kiran farko har tayi Ringing ta katse bai ɗauka ba. Sai na sake kira a karo na biyu. Jikina a sanyaye da tunanin ko fushi yayi. Bayan ta shiga Caraf naji an ɗauka. Ga mamakina sai naji saɓanin abinda nayi zato daga gareshi.
Muryarsa cike da Izza da Ginshira irin na Cikakkun mazan da suke amsa sunan Maza.
Yace. "Assalamu Alaikum! Sweetie Na! Ina kika shiga kika bar wayar nayi ta kiranki don naji ya jikin Yaya Taneem ɗin, kuma in kina Asibitin nazo nima na dubashi ni da abokina Uwais. Amma nayi ta kira baki ɗauka ba. Har Wayar Uwais ɗin na Karɓa na gwada kiranki da shi duk baki ɗauka ba".
Zuciyata tayi Sanyi. Yayin da raina yayi fari fes! Saboda jin bai min abinda na zaci zai min ba.
Don haka na lumshe ido gami da lanƙwashe murya cike da Kissa da Kilbasa irin tamu ta Matan da suke amsa sunan mata.
Nace. "Rabin Raina! Wallahi ba nisa nayi da wayar ba. Sha'afa nayi lokacin da zanyi Sallar Magriba na saka wayar a Silent. Amma kasan ai duk da na sha'afa zuciyata da Ruhina cike suke da tunaninka duk bayan ko wane second".
Ya bushe da dariyar jin daɗi. Yace.
"Na saba jin waɗannan kalaman daga wajenki tun ranar da muka haɗu da Junanmu. Muka amince zamu yi rayuwa irinta Laila da Majnun. Don haka ina buƙatar jin wasu sabbin kalaman daga wajenki".
Nayi dariya nima mai cike da kissa. Nace.
"Rabin Raina! Ai kasan kana Raina Kamar Kuɗin Haya! Beside ma fa nasha faɗa maka ko numfashi naja na sauke tunaninka damfare yake fall cikin zuciyata".
Ya sake Sheƙewa da dariya kamar wani Boss. Ina Jinsa yana tsallen farin ciki da murna akan gadonsa.
Yace. "Sweetie Na! Kin san wani abu kuwa?".
Nace." A'a sai ka faɗa!".
Yace. "Wallahi ji nake kamar idan wata ƙaddarar ta gilma ban aureki ba. Zan iya rasa raina! Bana fatan hakan ko kaɗan ma. Insha Allah kece Mace Ɗaya Tilo da zan mallaka a duk Tsahon rayuwata. Ki haifa min Yara guda Huɗu kyawawa masu Kama da Ke. Biyu Maza! Biyu Mata!....".
Na katse shi ta hanyar sheƙewa da dariya nima.
Nace. "Rabin Raina! Nima ina jin abinda kake ji a cikin raina. Amma kuma haihuwar har da zaɓe?. Kuma Yara masu kama Dani? Ina ma laifin ace biyu suyi kama dani. Biyu kuma suyi kama da Kai?.
Yana dariya yace.
" To ai nafi ƙaunarki ne fiye da yadda nake ƙaunar kaina. In kuma baki yarda ba gobe kice na rungumi Transformer ki gani idan nazo wajenki da Yamma zaki ga abinda zan aikata. Saboda soyayyarki".
Na kwashe da dariya har ina ƙwarewa.
Nace. "Kai Rabin Raina! Bar faɗin haka. Rai ai yafi komai. Za dai kayi wani abin akaina amma banda kisan kanka. In ka kashe kanka kuma ai ka rasa ni. Ko kuwa dai wayo ne da son kaje Aljanna ka samu Bonus na Hurul-ain guda dubu Saba'in?".
Yana Dariya Shima yace.
"Ko kaɗan Sweetie Na! Ai ni ko a Aljannar da za'a bani zaɓi zance a barni da ke kin isa ke kaɗai!".
To Haka dai muka raba dare muna musayar kalaman soyayya ni da Rabin Raina Musayyib Bala. Daga ƙarshe muka rabu cike da nuna tsananin ƙaunar juna.
*****. *****. *****
Abinda ya bani mamaki shine fiye da kaso 85 cikin ɗari na mafarke-mafarken da nayi a barcina. Maimakon nayi mafarkin Rabin Raina Musayyib sai na tsinci kaina da Mafarki da mutumin da ya zubar min da Abinci. Abin takaicin har a cikin mafarkin ban ga fuskarsa ba. Amma naga wai Ya min Kyautar Fure! Ya miko min ta bayan kafaɗunsa. Tashin hankali. Wannan fa shine; Amrul Azeem!.
Da Asuba bayan nayi sallah na zauna akan Dardumata ina Lazimi gami da Neman Tsari da dukkan sharrin dake tattare da wannan Mutumin da na haɗu dashi tunaninsa har yake neman ya sanya min damuwa.
Bayan na Kammala naje na Gaida Abbanmu da Mamanmu. Na Shiga Kitchen don taya 'yar aikin Gidanmu Baba Ɗahare aiki.
Al'adar Gidanmu ce bamu cika Sakarwa 'yan aiki, aikin gidan gaba ɗaya ba don gadarar muna biyansu. Mu kan taimaka musu. Wani wajen mu gyara musu ko mu kama musu. Hakan na sawa mu ƙaru da juna a fannoni dabam-dabam na aikin. Inda muka kula suna da naƙasu wajen gyara ko tsaftacewa sai mu koya musu. Su kuma inda suke da ƙwarewa sai su nuna mana. Don haka Alhamdulillah! Mun iya girki kala-kala na Gargajiyar Hausa da Wasu Yarukan gami da Na turawa da Larabawa ( Ma'ana dai Girkin zamani).
Bayan mun gaisa da Baba Ɗahare. Na tambayeta me yau zata Girka mana muyi Break-Past dashi. Tace tun jiya da dare ta haɗa kullin Wainar Shinkafa. Don ta Kula Alhaji na son wainar shinkafar da miyar taushe. Nace to kin tanadi abinda za a sha ko kuwa dai wainar kawai kika shirya yi? Tace ita Kaɗai tunda na Kula ba Koko kuke son sha ba. Sai ku haɗa da shayi ku sha.
Na Bushe da dariya nace.
"Baba Ɗahare Manya! Bari na tayaki aikin. Amma zan canja miki tunani kin san komai ana son a dinga zamanantar dashi. Ɗauko min Kullin na gani.
Ta Ɗauko min Kullin Wainar. Har ya tashi. Nace to ta Samo Wake Kamar tafin hannunta ta jika. In yayi laushi ta cire hancin ta sa min a Blender. Ni kuma na ɗauki sukari da Gishiri kaɗan na zuba. Har Curry da Albasa Yankakka na zuba. Na ɗan Kwankwatsa Tattasai duk na zuba. Ta kawo Waken ɗan kaɗan data malkaɗa a blender na zuba. Na ƙara Baking Powder. Tana kallona tace wannan Masaa kenan ko kuma wane sabon salo ne. Ni Ɗahare ban taɓa jin inda akai masa aka zuba Wake ba. Yau naga Duniya. Ina Dariya nace Baba Ɗahare. Kunna Gas ki fara Suya. Bari na Haɗa miki miyar kuma da za a ci Masar da ita. Sannan kuma yau ba da Tea zamu haɗa Masar ba da Kunun Coucous zamu sha me haɗe da Kwakwa.
Baba Ɗahare tace. "Duniya! Ban taɓa jin in da akai kunun coucous bama bare har da Kwakwa. Ku daman 'yan zamani kun fiye ƙaƙale-ƙaƙale. Shi yasa idan aka kaiku gidan tsohuwar mace ko ballagaza wacce bata iya girki da Kwalliya ko iyayi ba nan da nan kuke fitar da ita daga gidan. Yo! Ina Mazan wannan zamanin zasu iya zama da Sakaryar macen da bata iya girki ko gyara jikinta ba?. Ai duk namijin da kika ga Ya zauna da mace a haka sai dai ko kuɗinsa ne bai kai ba. Ko kuma Ƙaddarar haihuwar 'ya'ya ce ta zaunar da macen".
A haka muka cigaba da hirarmu muna aikinmu.
Baba Ɗahare tayi ta mamakin yadda wainar shinkafar take ta ƙamshi gashi tana tashi kuma cikinta babu Tuwo-Tuwon nan. Tace lallai yaran zamani baku da dama.
Na Kammala Kunun Coucous na Gurza Kwakwa na zuba. Na dama Madara na saka da Fulawa. Na ɗiga Flavours. Na Juye a Flask!.
Ɓangaren Miya. Nayi Miyar Water-leaf da Ogu. Na sanya Kifi Busasshe da Jelar Saniya da muka adana a Fridge Wankakkiya daman ta Jiƙu. Nan da nan Kitchen ya ɗauki Kamshi.
Na je na Watsa Ruwa a jikina don fidda Ƙaurin kitchen daga Jikina.
Sai Bayan na fito daga wanka ne. Ina gaban Madubi ina shafe-shafen kayan kwalliya. Sannan na tuna fa ashe jiya Mahfuzah ta kirani. Don haka na ayyana a raina in na gama Kwalliya zan kirata. Amma nasan sai nasha Mita da Gori a wajenta. Cewar ta Kirani har sau uku bana kusa da Wayar. Kuma dana dawo naga kiran ba zan iya kiranta na faɗa mata uzurin da ya hana ban ɗauki wayarta ba ko da bana kusa. Sbd rashin muhimmancinta a wajena. A raina na shirya amsar da zan bata.
Bayan mun kammala Break-Past ne. Ina Shirin Neman Mahfuzah a waya sai ga kiran 'yar halal!.
Na ɗauka nace.
"Ƙawalliya Romon Jaɓa! Afuwan! Jiya naga kiranki very late saboda nayi nisa da wayata ne kuma tana Silent".
Tace. "'Yar rainin hankali sabon sunan da kika bani kenan saboda rashin muhimmanci na a wajenki ko?. To me yasa baki kunna datar ki ba kuma tun jiyan. Na miki magana a WhatsApp na miki a Instagram ke har a Facebook messenger ɗin ki na miki Massage amma ban ga alamar kin buɗe datar ki bama".
Ina dariya nace. "To Alhamdulillah! Tunda ma kin kula da hakan. Jiyan ne na zama Very Busy wlh shi yasa nayi nesa da wayata".
Tace. "To daman kiran da nayi miki jiyan shine yau in kina da lokaci zanzo muje Gidan Zuhrah Khaleel kin san ta haihu an mata CS an fiddo mata Tagwayen yara. Yau wajen 2 Weeks kenan. Itama Yar rainin hankali bata faɗa ba sai Jiya a Group na Makaranta. Daman dai kamar ta kwana biyu bata hawa online".
Nace. "Allah Sarki! Tana gida ko tana asibiti?".
Mahfuzah tace. "Tana Gida. Ai kwana Shida da yin CS ɗin aka sallameta".
Nace. "To bari zan sanar da Mama idan ta barni zan faɗa miki sai ki biyo min da azahar muje. Sbd kin san yau ina sa ran zuwan Rabin Raina! Musayyib. Don haka bana son nesa da gida daga anyi Laasar don tanadar masa abinda zai ci idan yazo".
Taja tsaki. Tace. "Ke dai 'yar wahala ce. Wallahi ba a haifi Saurayin da zan dinga yiwa irin wannan bautar ta girke-girke da wani ɓata lokaci ina masa lemuka kala-kala yazo ya cika tumbinsa ya kaɗe rigarsa ya tafi ba. Ba wahala nazo yi duniyar ba".
Na Ƙyalƙyale da dariya. Nace. " Ai daman ke Hutsuwa ce. Cikin mata irinku baku da Yawa. Don haka ne ai Kullum kuke cikin Rigima ke da Mahboob ɗinki. Don ma yana mutuwar son ki. Amma da tuni ai gayyarku ta watse. Gashi an gama shirin aure".
Tace. "Kar ma ya so nin mana. Ya ga in wani bai so ni ba. Ga maza nan da yawa a gari kamar Ledojin Pure Water a Kano".
Nayi Dariya. Nace. "Waɗannan mazan da kike gani. Wasu da nasu su. Wasu kuma suna da wuyar Sha'ani irinki. Ai kin san dai Namiji ba Yadin Shadda bane da zaki je kantin Kwari kice a Yanko miki daidai da Wanda zai isheki dinkawa ki sanya a jikinki ba ko?".
Tace. "Kinga kar ki isheni da surutu kije wajen Mama Ki nemi izninta. Nan da Anjima zanzo na daukeki a motata mu je dubiyar. Don kin san ba zan shiga motarki ba. Kiyi ta yiwa mutane tuƙin slow kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Wai anya kuwa ma kina da Driving License kuwa?".
Ina Dariya nace. "Yar arufta! Daman ina zaki yi Driving License nima kuma nayi. Ai irinku 'yan arufta ake yiwa ba mu ba masu tuƙi da nutsuwa".
Muka Bushe da dariya muka katse Wayar.
****
Cikin Ƙawayena na Sahun gaba-gaba ina Ji da Mahfuzah. Sai dai Halinmu ba ɗaya ba. Ita Hutsuwa ce. Mai Zafi. Bata son Raini kuma bata Iya Lallaɓa mutum ba. Halinta wanda nafi so shine Mahfuzah bata munafunci kuma ba ayi mata ta Ƙyale. Tare mukai Secondary School a Model. Haka nan tare mukai University Abuja. Ajinmu ɗaya don haka Shaƙuwarmu ta Ƙaru. Har Iyayenmu mun haɗa suna zumunci.
Karfe Ɗaya na Rana Mahfuzah ta biyo ta ɗaukeni zuwa gidan Zuhrah mu dubata gami da yi mata Barka. Nace Mahfuzah mu biya ta Sahad Stores dake Area 11 mu siya mata kayan Barka tunda kinga dai ba ma je mata hannu haka ba.
Mahfuzah ta gallamin harara sanda nake shirin zama a kusa da ita a gaban mota. Tace.
"To uwar iyayi. Ba kuɗi sosai a Jakata. Kuma ban fito da ATM Card ɗina ba. To mene don munje mun dubata hakan? Shi ma ai arziki ne wani yaje ne?".
Nace akwai kuɗi a Jakata kuma na fito da ATM muje sai na siya mana duka.
Mun tsaya a Sahad Stores mun Siyi kayan Barka. Mun siyawa Babies Kayan sawa da Powder da Oils da Pampers. Ita Kuma Zuhrah muka siya mata Atamfa da Turaren Humrah. Aka saka mana a ledoji masu tambarin kamfanin.
Mun fito muna tafiya a harabar Sahad Stores ɗin kafin mu isa wajen da mukai Parking motarmu.
Muna tafe muna hira har da Rangaji. Kawai sai muka ji an ratsa ta Tsakiyamu kamar an bangajemu ma. Cikin Gudu-Gudu Sauri-Sauri an wucemu. Yayin da ledojin hannunmu suka faɗi har wasu kayan suka tarwatse a ƙasa.
Kafin mu dawo cikin hayyacinmu tuni mutumin da ya bangajemu ya mana nisa. Amma na kula da ƙirar jikinsa tabbas yayi kama da mutumin nan na jiya.
Mahfuzah ta kalleni tace." Wannan wane irin Ɗan iskan mutum ne. Yana kallon mata na tafiya ya rasa hanyar da zai wuce sai ta tsakankaninmu. Kuma yana ji ya bangajemu har ya zubar mana da kayan da yake hannunmu amma ya kasa tsayawa ya bamu Haƙuri?. Me yake ji dashi? Me yake taƙama dashi?. Wallahi sai...
Na sa hannu na rufe mata baki nace.
" Jiya ma ya zubar min da abinci. Watakila ko ni ya gane. Kuma akwai abinda yake ransa. Amma Maza Muje mu same shi wajen da ya nufa tunda muna hangensa".
Ai kuwa da hanzari muka nufi wajen da ya nufa inda yayi Parking motarsa.
Dai-dai lokacin da muka kusa isa wajensa tuni har ya gama fitowa cikin tsakanin motoci ya nufi wajen fita. Muna da tazara kuma mu a Kafa muke don haka ko kafin mu karasa tuni har ya fice daga harabar wajen.
Mahfuzah ta yi ƙwafa tace. "Wallahi da mun riski mutumin nan da sai ya raina kansa don sai na faɗa masa maganganu masu Yaji Marasa Sugar. Ya tabbatar da cewar mutane ya bangaje ba Karnukan gidansu ba marasa daraja.
Jikina a sanyaye nace. "Zan baki labarin yadda mukai dashi Jiya. Bari na tsaya anan je ki dauko motar mu tafi a hanya zan baki labarin duk yadda mukai".
Larabi ma ana yake cewa ku jirashi har zuwa lokacin da Mahfuzah zata ɗauko motar sai Ya cigaba da ɗauko muku rahoton yadda zata kaya.
Don jin Yadda zata Kasance. Tare kuma da Sanin Amsoshin tambayoyin da Sanin Amsarsu sai LARABI. Mu haɗu a rubutu na gaba.
Ɗan'uwanku. Ƙaninku. Abokinku. LARABI.
08065418892.
Ga masu son Littafin zasu iya biyan N300 Kacal. Za a sanya su a group na WhatsApp duk sanda aka rubuta a tura musu.
Idan kuma mutum yana son Ainahin littafin ne. Zai iya yin Booking @ N1000.
Abdullah Jibril
0162440684
GTBank
Wasu Labarai
0 Comments