An karanta wannan labari tare da yin bitarsa wajen Reading Session da Kungiyar Marubutan Jihar Katsina KMK ta gudanar a ranar 12 ga watan Febrairu, shekara ta 2022.
Yaran na riƙe a hannunta
babban zai kai shekaru biyar, mai bi mashi kuma Shekaru huɗu, yayin da wanda
take goye dashi zai kai shekaru biyu.
A Siffa ta jiki ba za a kira
Jamila da mabaraciya ba, sakamakon babu alama ko ɗaya a jikinta da zata nuna
tana cikin wani hali, na neman taimako amma kuma taimakon take nema.
Gidan mai ta nufa da yaran
sakamakon hango cunkoson jama'a ta san ko babu komai zata iya samun sadaka a
can.
Daidai fakawar Fahad a wajen
da motar shi 206 Baƙa. Ya bi layin jama'a shima domin ya sha mai. Ya sauko da
gilashin motar ne daidai saitin da yake domin kallon jama'a kafin layi yazo
kansa.
Ya hango Jamila macen da bai
kamata ace tana a rana irin haka tana bara, abun mamaki ya kama shi, ba ta yi
kama da mai bara ba. Ya nutsa da mamakin dalilin da yasa take bara sai gashi ta
tunƙaro inda yake.
Yaron da shekarun shi basu
wuce biyar ba ya fara magana;
"Alhaji Allah ya tsare,
A taimaka mana da sadaka mu
'yan Gudun Hijira ne"
Da alama waɗannan
kalmomi yaron ya haddace su sosai a kan shi, sakamakon maimaita su da yake ta
yi.
Fahad ya kira uwar da hannu.
Ta matso sosai kamar zata buɗe
motar ta shiga, sannan ya ce;
"Zaki iya aikin Abincin
sayarwa ana biyanki?"
Jamila ta amsa da sauri ta
ce,
"Alhaji Me zai hana?
Wanda ya faɗa ruwa ai ko takobi ka bashi kamawa zai yi, wannan barar da nake
gararambar yi da yara a titi ai ba don ina so nake yi ba, In san samu ne ace
ina gida ina sana'a su kuma suna makaranta, ɓarayi sun kashe mani mahaifinsu,
ni kuma sun sa mun gudu mun baro muhallinmu, barar ce abu na ƙarshe da zan yi
in ciyar da yaran nan".
Ta duƙar da kai ƙasa sai
hawaye.
Fahad ya kai Jamila gidan
wata yayarsa mai sayar da abinci da ya ji tana neman 'yar aiki, aka kuma yi sa'a
ta ɗauke ta.
Da yake Jamila mai ƙoƙari da
ƙwazo ce da abincin da take samu take ciyar da yaranta, kuɗin da ake bata dasu
ta saka yaranta biyu Islamiyar Unguwar da ake biyan kuɗin sati. Da makarantar
Gwamnati ta boko.
Daga nan rayuwar Jamila da
yaranta ta gyaru, cikin ƙanƙanin lokaci ta goge, a gidan matar nan da suke
sana'ar abinci ta samu miji, wani mai rufin asiri ya aure ta, bayan bincike da
ya yi a kanta da kuma tausayi da take bashi, ya ɗauki nauyin karatun yaranta su
uku.
Ba zamu iya
kawar da bara ba, duk yadda muke tunani, amma zamu iya ba mabarata gudummuwa ta
hanyar gyara rayuwarsu, kamar yadda Fahad ya yi.
Zagi, tsinuwa
ko ƙananan maganganu kan mabarata Mata da Maza ba zai zama mafita ba, wasun sau
da yawa in zaka ji sanadin bararsu dole ka tsaya ka kai masu ɗauki.
***
0 Comments