Talla

Littafin Gidan Darling (Page 1) Na Larabi

 Wannan taɓa ka lashen Kyauta ne. Amma ga mai son jin cikakken labarin littafin za a biya kuɗi kaɗan.

TAƁA KA LASHE....!

Mijina ba wani kyakkyawa bane na bugawa a Jarida. Amma yana da kyau daidai nasa.

Yana da siffar cikakkun maza. Yana da haiba da muhibba.

Baƙi ne ko nace wankan tarwaɗa kamar yadda mu Hausa-fulani mukewa masu duhun fata alkunya.

Yana da faɗin kafaɗu da gashi a fuskarsa tun daga qasumba har saje da gemu.

Gwanin iya kwalliya ne musamma da yake ma'abocin sanya ƙananan kaya ne.

Sauban Mahmoud sunansa. Mun haɗu dashi a babban asibitin kwararru na maitama distric dake abuja.

A matattakalar bene ina gaggawa zan kaiwa Anti Yusrah abincin ranarsu. Kasancewar na makara kusan 5pm a lokacin.

Yana hanzari cike da ruɗewa kamar wanda baya gani ya kifar mani da boxes ɗin abincin.

Komai ya tarwatse hatta fruit salad ɗin dana haɗa masu wanda na fi ɓata lokaci a kansa saboda ina da yaƙinin Uncle Taneem   zai sha wanda shi ne mara lafiya.

Ga mamakina sai na ga bai tsaya ta kaina ba. Kawai ya yi wucewarsa cikin gudu-gudu sauri-sauri kamar yadda ya tunkaroni.

Haushinsa da takaicinsa suka ƙumeni a cikin zuciyata.

A raina na ce wannan wane banzan mutumi ne zai mani asara kuma bai tsaya ya bani haƙuri ba bayan yana ji ya zubar mani da abincin da nake ɗauke dashi har miya ma ta fantsama a jikin kayansa.

Nan da nan shaiɗan da zuciya suka tunzurani. Nima na bar kayan da ya ɓare a wajen na ce wallahi ko shi wanene sai na bishi na ga abinda yasa ya zubar mani da abinci kuma ya kasa tsayawa ya bani haƙuri. Na ji da me yake gadara?.

Ai kuwa na buga tsalle na take masa baya. Kasancewar ya rigani yin gaba kuma yana tafiya da sauri mai kamar gudu yasa na kasa cimmasa har ya gama sauka daga benen ya gangara can ainahin farfajiyar asibitin.

Yana tafe ina binsa a baya. Amma da yar tazara a tsakanimu.

Saurinsa ya katse gaban wata mota dark ash color. Ya yi hanzarin buɗe motar sai na ga ya shige da sauri ya tada key. Yayi reverse ya figi motar da gudu sauran kaɗan ya take mani ƙafa.

Na tsaya sororo jikina duk a mace. A fili ba a ɓoye ba, na ce,

"Amma gaskiya wannan mutumin duk yadda a kai akwai babbar damuwa a tare dashi, kuma bai kamata a barshi ya tuƙa mota cikin wannan yanayin da yake ciki ba".

Don haka na tsinci kaina da son binsa na ga me yasa yake ta wannan gaggawar.

Cikin zafin nama nima na tunkari motata wadda ba nisa da inda nake tsaye. Na yi hanzarin shiga na bi bayansa.

Nayi sa'a ina fita na hange shi saboda traffic da ya dakatar dasu. Don haka na kurkurɗa gefe da gefe har na kusa cimmasa illa akwai tazarar motoci tsakaninmu amma ina ganinsa.

Ai kuwa traffic na bada hannu ya figi motar da gudu nima kuwa na rufa masa baya.

Cikin wasu yan mintuna sai gamu a tsakiyar wuse 2. A wani layi Agadez Cressent.

Ya nufi wani tamfatsetsen gida. Nan da nan na ga gateman ya wangale masa gate ya faɗa da hanzarinsa.

Na yi turus. Ni ba abin na shiga ba, kar ace je gidansa ne. ,u kwashi 'yan kallo da matarsa. Ko kuma gidan yankan kaine yasa a gille mani kai.

Na ja can gefe sosai nayi parking daf da gidan.

Nan da nan na ji wayata ta fara ringing na laluba yar poss ɗina na jawo wayar sai na ga kiran Anti Yusrah.

Sai yanzu nima hankalina ya dawo jikina na ce, tabbas na tafka babban kuskure na bar Anti Yusrah da mara lafiya ba abinci tun tea ɗin safe, gashi na zo abincin ya zube. Wanda ya zubar bai tsaya ya bani haƙuri ba. Nayi ɗanyen kai na biyo shi, gashi ba riba ya shige gida ya barni.

Ina tsaka da wannan tunanin ne wayar ta katse. Yayin da kuma na fara jiyo ihu da kururuwa daga gidan da wannan wanda ya ɓarar mani da abincin ya shiga. Kuma da alama ba ihun mutum ɗaya bane.

Zuciyata ta cika da tsoro na ce wannan ihun mene ne? Na mutuwa ne ko ihun mene ne?.

Nan da nan wani ɓangaren na zuciyata ya bani shawarar na yi sauri na bar wajen kar wani abu ne ya faru azo a haɗa dani banji ban gani ba. Saboda jin dalilin me yasa aka zubar mani da abinci.

Cikin sanyin jiki na murda sitiyarin motata na canja giya zuwa D. na harba bisa titi. Na nufi kantin kwalam da makwalashe, na yi order abinci take away na nufi asibitin don kaiwa su Anti Yusrah madadin abincin da na kawo masu wannan banzan mutumin (haka na saka masa a zuciyata).  Ya zubar mani kuma yaƙi ya tsaya ya bani haƙuri.

****

Anti Yusrah ta galla mani harara gami da hayayyaƙo mani da cewa,

"Haba Nuzlah! Kamar baki san mutane ki ka ajiye a nan ba. Na ce maki by 2:30 to 3 pm ki kawo mana dinner amma har sai yanzu da ki ka ga dama za ki kawo mana dinner around 6'oclock?

Wato sai kin gama chatting da samari da kawayenki  sannan za ki kawo mana abincin ko?"

Jikina a sanyaye, na ce

"Wallah Anti Yus....."

Ta katse ni da cewar,

"Dallah rufe mani baki, halinki ne ban sani ba? Yanzu kuma kina so kiyi mani musu da shegiyar ƙarya ko?".

Ina sosa kaina wanda ba wani ƙaiƙayi yake yi mani ba, illa kawai salo ne na maras sa gaskiya.

Na ce,

 "Kiyi hakuri Anti wallahi wani mutumi ne ya zubar min da abincin. Ina shigowa cikin asibitin har na kusa karasowa, a matattakalar bene, kuma bai tsaya ya bani haƙuri ba. Shi ne na je na siyo maku wani abincin don na ga lokaci ya ƙure".

Anti Yusrah ta buɗe baki galala gami da kama haɓa tana kallona tama rasa bakin furta wata maganar...

Larabi ma nan ya buɗe baki galala. Har wayar da ke hannunsa da yake ɗauko maku rahoto da ita taso ta suɓuce ta faɗi.

Zan cigaba da kawo maku rahoton abubuwan da suka faru a rubutu na gaba.

Don jin yadda zata kasance tare kuma da sanin amsar da sai Larabi ya san ta, mu haɗu a rubutu na gaba.

Ɗan'uwanku, Ƙaninku, Abokinku Larabi

Wasu Labaran Hikayata

  1. Mugun Boss (Mayaudari): Sister Iyami 
  2. Hattara Da Bestie: Sister Iyami
  3. Mutum da Muhallinsa: Bello Hamisu Ida

Post a Comment

0 Comments