Talla

Da Gaske Ne Yau Za a Ɗaura Wa Aisha Tsamiya Aure?

 Daga: Hauwa'u Bello



KANO, NAJERIYA - Jiya ne aka ta shi da wani raɗe-raɗen cewa ranar juma’a za a ɗaura wa shaharariyyar yar wasan film ɗin nan mai suna Aisha tsamiya aure, kodayake ta karyata zancen raɗe-raɗin, inda ta ce, har yanzu da sauran lokacin aurenta, jarumar ta tabbatar da cewa ba gobe ne za a ɗaura mata aure ba sai nan gaba.

Batun ɗaura aurenta ya karaɗe kafafen sada zumunta kamar wutar daji, inda aka riƙa yaɗa wani katin gayyata mai ɗauke da sunan jarumar aka kuma bayyana cewa ranar ashirin da biyar da wannan ta ne za a shiga da ita daga ciki.

An bayyana sunan mijin da zata aura mai suna Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.

Bayan ganin katin gayyatar, masoyanta da abokai da aminai da kuma abokan sana’arta suka fara yi mata Allah san barka da fatan alƙairi, wasu ma daga cikin abokanta da ‘yan uwa da abokan sana’arta da kuma masoyanta sun taya yaɗa hotunan a shafukansu.

To Aisha Tsamiya ta rubuta a shafinta na Instagram inda ta yi ƙarin bayani da cewa,

 “Assalamu alaikum, jama’a barkanmu da warhaka. Na gode da addu’o’inku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, amma aure na ba 25th ga wannan watan ba ne, sai neɗt month in-sha Allah. Na gode Allah ya saka da alkhairi.”

Wannan sanarwar, wadda Tsamiya ta yi a shafin ta na Instagram mai mabiya sama da miliyan ɗaya, ya ba mutane da dama mamaki, haka kuma ya sake buɗe masu wani shafi. Kodayake a cikin sanarwar Aisha bata ƙaryata zance yin auren ba, saidai da faɗi asalin lokacin yin auren inda ta ce sai wata na gaba.

 ‘Yan shekarun baya har an gama maganar auren ta da wani attajiri da ke Jihar Kebbi, wanda aka sa bayan ta dawo daga aikin Hajji za a yi bikin, ta na dawowa sai kuma labari ya canza, aka fasa auren. Wasu na cewa ita ce ta ce ta fasa auren, yayin da wasu su ka riƙa cewa shi ne ya fasa saboda wasu dalilai.

Kafin wannan lokaci, an ɗauki tsawon lokaci ba a jin ɗuriyar jarumar a Kannywood, musamman a yanzu da masana’antar ta koma cin kasuwa a YouTube.

Post a Comment

0 Comments