Daga: Hauwa’u Bello
KANO, NAJERIYA — Maryam
Yahaya ɗaya daga cikin ‘yar wasar Kannywood wadda ta taɓa samun kambun zama
fitacciyar yar wasan kwaikwayo ta City People Entertaiment a shekarar 2017, ta
fara shahara a cikin fim ɗin Traddadi.
Maryam ta fara sha’awar shiga
harkar fim tun tana yarinyar ƙarama, ta fito a cikin fina-finan Gidan abinci da
Ɓarayuniya da Tabo da Mijin Yarinya da Mansoor da Mariya da Wutar Kara da Gidan
Kashe Awo da Gurguwa da Mujaddala sai kuma sabon fim ɗin ta tayi na
kwana-kwanan mai suna Lamba wanda ta yi bayan ta tashi daga matsananciyar
rashin lafiya.
A kwanakin baya ne Maryam ta ɗauke
ƙafarta daga harkokin fim, har na tsawo lokaci bayan fama da tayi da rashin
lafiya. Kodayake gabanin rashin lafiyarta masoyanta da sauran mutanen sun yi ta
tofa albarkacin bakinsu, inda wasu ke mata fatan samun sauƙi, wasu kuma na
tarabbabin ainin irin rashin lafiyar da take fama da ita.
An dai ji ta bakin mahaifinta
wanda ya shaida cewa, Maryam ta yi fama da zazzaɓi ne wanda ya ja har ta kwanta
asibiti amma daga bisani ta samu lafiya. Saidai wasu waɗanda basu shafi
rayuwarta ba sun yi ta ƙara gishiri a cikin rashin lafiyarta, wasu har ma suna
alaƙanta rashin lafiyarta da shafar jinnu wasu kuma ganin cewa jifa aka yi
mata.
Koma dai meye, da yawa daga cikin
waɗanda suka yi mata fatan samun sauƙi, cikin ƙadartawa da ikon mahalici ta
samu sauƙi har ma ta koma facen shirya fina-finai.
Saidai kafin ta koma shirya fim,
wasu sun sha jawo hankalinta a kan ta fita daga harkar fim saboda tsallake
rijiya ta baya da tayi, wasu kuma na ganin kamar cewa ta yi saurin dawowa
harkar fim da wuri, amma dai tun da sana’a ce ta ke yi, koma dai ya wasu za su
kalli abun, ba za ta yi sako-sako da sana’arta ba.
Bayan fama da rashin lafiyarta,
da warkewarta, an fara ganinta a shafin TikTok inda take yin hotuna da bidiyo
tana wallafawa a shafinta, taga bisani kuma sai ta ci gaba da harkar fim ɗinta
inta ta fito a cikin shahararren fim ɗin Lamba, wanda kamfanin Daudau Kahutu
Rarara ya shirya.
0 Comments