Talla

Baya Ba Zani: Karancin Man Fetur A Arewacin Najeriya

 Daga: Hauwa'u Bello



ABUJA, NAJERIYA - Tsawon wata ɗaya kenan da ‘yan Najeriya ke ta fama da ƙarancin man fetur, wanda ya taimaka sosai wajen hauhawar farashin kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa. A wasu jahohin farashin man fetur ya haura naira ɗari uku a duk lita ɗaya. Wasu gidajen man kuwa su kan saida leta a kan naira ɗari biyu da talatin ko da arba’in, ya yinda galan ɗin mai yake kamawa dubu ɗaya da ɗari shidda ko ma abinda ya fi haka a kasuwar bayan fage.

A garuruwan Katsina da Kano da Sokoto da Zamfara da Kaduna da Jigawa da Bauchi da sauran garuruwan Arewacin Najeriya kai har ma da sauran garuruwan Kudancin Ƙasar ana shan wahala sosai kafin a samu a sha mai a gidajen mai, bayan kuma an zo sha a kan samu man ya yi tsada sosai inda ya haura naira dari da sittin da biyar wato farashin da gwamnati da saka a saida man fetur.

Wani mai tuƙa keke-napep wanda ya buƙacia  sakaya sunansa ya shaida wa Arewa News yadda yake shan wahala kafin ya samu man da zai yi aiki da shi, ya ce, idan ya fito da asubahi a gidan mai yake samu ya yi sallah, haka kuma kafin ya je gidan man sai ya yi ta buga waya don ya tabbatar da cewa an kawo mai kuma ana saidawa a gidan man da zai nufa.

Ya ƙara da cewa, idan ya je sai ya bi layi, a nan zai yi sallah asuba zuwa asahar wani lokacin ma har sai ya yi la’asar sannan zai samu shan mai. Kuma ya kan sha man da tsada. Don  haka bayan la’asar ko gefen magriba ne yake fara aikinsa na kabu-kabu. Kuma indai yana so ya maida kuɗi har ya samu na cefane dole sai ya ƙara farashi ga masu hawa kekensa.

Arewa News ta ji ta bakin ƁOA Hausa cewa, wani direba dake tuƙa tasi a garin Abuja wanda ya buƙaci su sakaya sunansa ya ce yana bin layi a gidan mai na tsawon awowi ashirin da huɗu kafin ya samu ya sha mai. (Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng

Wasu Labarai

Shugaba Buhari Ya Yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Bisa Ƙoƙarin Samar Da Ababen More Rayuwa

Shin da Gaske Ne Hushpuppi Ya Mutu?

Babu Wata Ƙaramar Hukuma A Najeriya Da Ke Ƙarƙashin Ikon 'Yan Ta'adda - CDS


Post a Comment

0 Comments