Wani bakauye ne ya yi abota da wani Iyamiri. Duk sanda ya shigo gari sai ya je wurin abokinsa su yi fira, haka shima Iyamirin yakan je kauyen
abokinsa su sha fira su ci abinci.
Rannan sai shi Iyamirin ubansu ya mutu a can garinsu, sai ya shirya ya tafi garinsu don a yi bikin rufe ubansa, amma bai sanar da wannan abokin nasa ba. sanda bakauyen nan ya shigo gari ya je shagon abokinsa sai ya tarar da shagon a rufe.
Koda ya tambaya sai aka faxa masa abinda ya faru da uban abokinsa, sai ransa ya baci kwarai ya koma gida.
Bayan Iyamirin ya dawo, da bakauyen nan ya shigo gari karo na biyu sai ya iske abokin nasa ya komo. Da suka gaisa sai ya ce wa Iyamirin,
"Wato babanku ya mutu a gida kun je garinku kun yi wasa kun ci abinci kun sha giya kun more amma baka gayyace ni ba, to bakomi ai ni ma babanmu yana asibiti"
0 Comments