Bayerabe ya ga wata Bahausa yana so ita kuma ta qi, sai wata rana ya ji wasu na cewa;
"So tsuntsu ne, yana tashi daga kan wata bishiya zuwa wata".
Sai ya ce,
"Hoh dama ashe so tsuntsu ne shi ne na tsaya ina wahalar da kaina a wajen wannan yarinyar, ga tsuntsaye da yawa a daji a banza”
Daga nan sai ya tafi daji, yana shiga daji sai ya ga wani tsuntsu ya tashi fir! Daga kan wata bishiya ya sauka a kan wata, yana ganin haka sai ya ce,
“yawwa”.
Nan take ya je wajen bishiyar da tsuntsuwa ta sauka, ya fara magana da bishiya wai a matsayin budurwarsa tun da dai so ya sauka a kanta wato tsuntsu.
Wasu Labaran Ban Dariya da Nishadi
0 Comments