Daga: Hauwa’u Bello
ABUJA,
NIJERIYA — NAN ta ruwaito Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar (CDS), Gen. Lucky Irabor, na
cewa, babu wata ƙaramar hukuma a Najeriya da ke ƙarƙashin ikon 'yan ta'addan Boko Haram ko ISWAP.
Irabor ya bayyana haka ne a taron Tarihi na ƙarni na 21 mai taken: ‘Tafiyar Karya: Yaƙi da Rashin Tsaro a Najeriya’
(Going for Broke:
Fighting Insecurity in Nigeria) a turanche, wanda ya gudana a ranar Laraba a Abuja.
Ya ce an kafa dokar ta-baci kan wasu ƙananan hukumomi a yankin Arewa maso Gabas a baya,
musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
A cewarsa matakin da aka ɗauka a wancan lokacin ya zama dole domin ƙasar ta tanadi ƙa'idojin tafiyar da irin wannan rikici.
Ya
ce,
"Duba waɗannan batutuwa, dole ne sojoji su aiwatar
da matakai ta hanyar ƙirƙira ayyuka don dacewa da abubuwan kowane yanki na
siyasa”.
Ya
ci gaba da cewa,
“Muna da Operation Lafiya Dole a yanzu
wadda ta ke yin aiki a Arewa maso Gabas, da Hadarin Daji wadda ke yin
aiki a Arewa maso Yamma
da haka kuma suna gudanar da ayyuka daban-daban a Arewa ta Tsakiya”.
Ya
ce,
“An sami farfadowar ayyukan jirage
sojoji dake aikin tsaro ta sararin samaniya. A daidai lokacin da ake tada ƙayar baya, ƙananan hukumomi 14 musamman a Borno na ƙarƙashin ikon Boko Haram amma a halin yanzu babu ko
ƙaramar hukuma ɗaya a hannunsu”.
“Haka ma a Yobe, kusan ƙananan hukumomi huƙu ne ke ƙarƙashin ikon Boko Haram da kuma Adamawa amma a halin yanzu
Boko Haram ba ta da iko da kowace ƙaramar hukuma”.
"Mun kwato makamai da alburusai hannun
‘yan ta’adda sannan kuma wasu ‘yan ta’addan Boko Haram sun miƙa wuya," in ji shi.
Irabor ya ce sojojin sun kwaci ɗimbin rundunar haɗin gwiwa ta farar hula tare da tura su yankunan da abin
ya shafa.
Ya ce, kashi 80 cikin 100 na jami’an rundunar a halin yanzu ana
jibge su a faɗin Jihohi 36 na tarayya wajen samar da tsaro da gudanar
da ayyukan ‘yansanda.
A cewarsa, wannan shi ne dalilin da ya sa ya shiga cikin masu ba da shawara ga
aikin al'umma.
Ya
kuma ce,
"Eh akwai tsarin aikin 'yansanda a halin yanzu, amma
dole ne a ƙara yawan jami’ai”.
“Hukumar NPF ta riga ta fara aiki a kan wannan don ganin
yadda za su haɓaka hanyoyin aikin ‘yansanda fiye da yadda take a yanzu”.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci tushen shigar mu,
kuma tushen rikicin cikin gida ne”.
“Tabbas, kundin tsarin mulkin mu ya umurci rundunar soji
da su taka rawar goyon baya ga hukumar farar hula, a wannan harka ta ‘yansanda,
a halin da muka tsinci kanmu”.
"An yi zaton cewa sojoji za su kasance a kan gaba wajen
magance rashin tsaro," in ji shi.
CDS ya kuma ce an siyasantar da ƙalubalen tsaro a ƙasar.
A cewarsa, siyasar tsarin aikin soja ya zama mai zurfi,
wanda ya sa kyakkyawar niyyar sojojin ta karkata.
Irabor ya ɗora alhakin rashin tsaro a ƙasar kan rikicin ƙasar Libya, wanda a cewarsa, ya kai ga ba da izinin
shigowa da makamai ta kan iyakokin Najeriya.
Ya yi kira da a ware ƙarin kayan aiki ga bangaren tsaro domin biyan buƙatun sojoji.
CDS ya ce Najeriya na sa ido a ciki don samun kayan aikin soji
don maye gurbin waɗanda ake shigo da su a hankali.
(Arewa News) www.arewanews.org.ng ko www.arewa.com.ng
Wasu Labarai
0 Comments