Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NAJERIYA — Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya da aka fi sani da sunan Academic Staff Union of Universities wato (ASUU) ta faɗi matsayarta a yau game da tafiya yajin aiki. Ana sa ran jin cikakken bayani daga ƙungiyar a kan ranar da zata fara yajin aikin wanda ta kira yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya.
Bayan kamala tattauanwarsu
da suke yi a yau, sun faɗi abinda suka tattauna
a kai da kuma tsayar da suka cimmawa. Wai jami’in ƙuniyar
ya tabbatar da cewa a yau ne za su yi ƙarin
bayanin abinda suka tattauna na tsunduma cikin yajin aiki na wata ɗaya.
Bayan tattaunawar da aka yi wadda aka fara tun da sanyin safiyar ranar Litinin, Majalisar
Zartarwa ta ƙasa, wato NEC, da ƙungiyar malaman
jami’o’I wato ASUU sun kaɗa kuri’ar fara yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya don amsa buƙatunta daga gwamnati.
Wata majiya a wajen taron da aka gudanar a
Legas ta shaida wa
Jaridar Vanguard cewa, yajin aiki ne wanda zai ba Gwamnatin Tarayya damar yin abinda ya dace.
Majalisar zartarwa ta
ASUU ta fara taron ganawa tun a daren Asabar a Jami'ar Legas (UNILAG), a wajen
taron ne aka cimma matsaya kan matakin da ƙungiyar
ta ɗauka.
Tun
a farkon watan nan na Fabarairu ne ƙungiyar
ta nemi dukkan jami'o'in ƙasar su ware rana ɗaya
ta hutu domin wayar da kan ɗalibansu game da
rashin cika alƙawari da gwamnatin Shugaba
Muhammadu Buhari ta yi masu.
Ta
ce har yanzu gwamnatin ba ta cika alƙawuran
da yarjejeniyarsu ta ƙunsa ba da suka ƙulla
a 2020, ciki har da maganar tsarin biyan albashi da kuma kuɗaɗen
gyaran jami'o'in gwamnati a faɗin ƙasar.
Al’amarin yajin aiki da jami’o’i ke yi a wasu lokutan ya zama barazana ga karatun ɗalibai inda mafi yawan karatunsu ke taɓarɓarewa, wasu daga nan ne ma silar karshen karatunsu, kodayake ƙungiyar tana ƙirƙirar yajin aikin ne don tabbatar da ingantacciyar rayuwa mai ɗorewa a jami’o’i.
Wasu Rahotanni
0 Comments