Daga: Muhammad Abdallah
SOKOTO, NAJERIYA -Ɓarayin daji masu
satar mutane don karɓar kuɗin fansa na ƙara kwarara a garuruwan Sokoto, inda
suke faɗaɗa hare-harensu. Wasu daga cikin ɓarayin na kwarara ne daga Kaduna ko Birnin
Kwari da Katsina da Zamfara. Ko a ranar talata saida aka kama wasu ɓarayi a
wani samamen da rundunar yansanda ta Operation
Sahara Storm ta kai, sun kama wani riƙaƙƙen ɓarawo wanda ya zo daga Jihar
Falato don sayar da makamai a Jihar Zamfara da Sokoto, haka kuma rundunar ta kama
wani riƙaƙƙen ɓarawo mai suna Musa Kamarawa wanda ke kai wa Bello Turji Makamai.
A ranar talata ne, wasu ɓarayi suka kai hari
a garin Ambarura dake ƙaramar hukumar Illela ta Jihar Sokoto, inda ɓarayin suna
sace mutane a gidan wani Basarake.
Ɓarayin sun shiga garin na Ambarura da
tsakar dare, bayan sun yi harbe-harshe suka kuma sace mutane tare a kwatar
dukiya da abinci da shanu. Ɓarayin sun shiga gidan Basaraken na garin Ambarura
inda suka sace yara da yanmata waɗanda basu wuce shekara goma sha uku ba,
sannan suka sace wasu dattijai.
Ɗanmajalisar dake wakiltar yankin wato
Honarabul Bello Isa Ambarura ya bayyana cewa,
“Mun daɗe mu
na fuskantar matsalar tsaro, musamman gabashin Sokoto, a garuruwa Gwadabawa,
Raba, Wurno, Isa, Sabon Birni na fuskantar hare-haren ɓarayin daji masu satar
mutane don karɓar kuɗin fansa, dukkan garuruwan suna bakin boda ne”.
Rashin tsaro
a Arewacin Najeriya ya yi ƙamari, lamarind ake sanya mafi yawan ‘yan Najeriya
yin barci da ido ɗaya. Kodayake Gwamnati da Jami’an tsaro na yin iyakar ƙoƙarinsu
wajen daƙile hare-haren ɓarayin da masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
Bello Turji na daga cikin shahararrun ɓarayin
da suke satar mutane don karɓar kuɗin fansa da kai hare-hare da saka haraji a
wasu garuruwa da tursasa hakimai da magadda da masu unguwanni su biya shi hara
shi. Ko baya-bayan nan saida ya saki wasu mutane da ya kama a yunƙurinsa na yin
sulhu da gwamnati. An dai taɓa ganin wata wasiƙa da ake zargin shi ne ya rubuta
inda ya nemi ayi masa sulhu don kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Garuruwan Katsina da Zamfara da Sokoto da
Kebbi da Kaduna da Nija na daga cikin Jihohin dake fama da ɓarayin daji masu
satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
Wasu Labarai:
0 Comments