Daga: Muhammad Abdallah
Zamfara, Najeriya - Majalisar Dokokin Zamfara ta cire Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu daga kukerarsa. Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ranar Laraba ta kaɗa ƙuri'a domin tsige mataimakin gwamnan jihar wato Barrista Mahdi Aliyu Gusau
Wajen kaɗa ƙuri'ar, ƴan majalisa 20 cikin 24 sun zaɓi a tsige mataimakin Gwamnan bayan wani rahoto da kwamitin shari'a a jihar ya gabatar a kansa da ya same shi laifi kan zarge-zargen da ake yi masa.
Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da suka halarci zaman Honarabul Ibrahim Tudu Tukur mai wakiltar Bakura ya shaida cewa, su 21 cikin 24 suka halarci zaman kuma mutum 20 sun amince da a cire mataimakin gwamnan daga kujerarsa.
Mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa an yi masa bi-ta-da-kulli ne saboda ya ki sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da gwamnan jihar.
Amma kuma, daga cikin dalilan da majalisar ta bayyana na tsige mataimakin gwamnan sun haɗa da rashin amsa gayyatar da aka yi masa ba, batun da Mahdi Aliyu Gusau ya ce an saɓa doka wajen bin ka'idar tsige shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi.
Wasu Labarai
0 Comments