Daga: Mohammad Abdallah
KANO, NAJERIYA — A Kano cikin unguwar Kadawa wasu
mutane da ake zargin ‘yan fashi ne sun shiga gidan wata mata sun kashe ta
sannan suka raunata ya’yanta, ‘yan fashin sun kashe matar ce wadda aka tabbatar
da cewa sunanta Ruƙayya, babu wanda ya san lokacin da aka kashe matar, saidai
an tsinci gawarta ne bayan an kashe ta jiya ranar asabar kenan da Magariba.
Mazauna yankin, sun tabbatar da cewa ba su ga lokacin da ɓarayin
suka shiga gidan ba, haka kuma basu ga fitar kowa ba, saidai maigidan mamaciyar
ya tabbatar da cewa, bayan ya dawo ne ya tsinci gawar matarsa kwance a mace. An
yi zargin cewa, ɓarayin sun kashe matar ne ta hanyar amfani da taɓarya sannan
suka jiwa ya’yanta biyu ciwo.
Rundunar ‘yansandan Najeriya ta Kano ta tabbatar da faruwar
al’amarin kuma ta ce tana gudanar da cikakken bincike.
Ko a watan daya gabata, saida wani malami ya kashe wata
yarinya mai suna Hanifa kisan da ya ja hankalin al’umma da dama a faɗin duniya.
Malamin Hanifa ya sace ta ne sannan ya bata guba ta sha, daga bisani ya binne
ta.
Kisan mutane dai a garuruwa Katsina da Kano da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Nija ya zama ruwan dare, saidai hukumomi da gwamnati da
jami’an tsaro suna iyakacin ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshen waɗannan kashe-kashe.
Wasu Labarai:
0 Comments