Daga: Muhammad Abdallah
KANO, NAJERIYA —
An samu wasu yara da suka kai kimanin 113 xari ta goma sha uku a wani gida dake
a unguwar Wailari Na’ibawa a qaramar Hukumar Kumbotso ta Kano, a wani gida da
ake zargin an kashe wani yaro tare da binne gawarsa.
Ta bakin SP Abdullahi Haruna
Kiyawa a wata zantawa da aka yi da shi da manema labarai a cikin makarantar ya
yi qarin bayanin yadda aka gano makarantar. Bayan sun samu wani rahoto a bakin
wasu mutane, bayan gwamnatin Kano ta hana gudanar da gidajen mari inda yawanci
ake azabtar da yara, akwai wasu mutane dake gudanar da irin wannan gida. Haka kuma
an samu rahoton cewa akwai yaron da aka azabtar dashi tare da bugun sa wanda ya
yi sanadiyar mutuwarsa, kuma wani malami da yake gudanar da gidan ne yasa aka
binne yaron ba tare da sanin iyayensa ba.
Bayan tuhumar wanda ke gudanar da
gidan, malamin ya yi iqirarin cewa yaransa dake makarantar karatu kawai suke yi
babu wanda ake azabtarwa.
Rundunar ‘yansanda ta tusa
qeyarsa zuwa makarantar sai aka samu wani waje da aka rufe yara wanda yawansu
ya kai 113 xari da goma sha uku, a cikin wani xan qaramin xaki, inda a nan ne
suke kashi da fitsari, ko ruwa ma in za su sha saidai su xebo na kewayen dake
cikin xakin.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya
qara da cewa,
“Yanzu haka dai an fara gudanar
da bincike, za ayi binciken da ya kamata, kuma duk wanda aka samu da zargi
musamman na mutuwar wannan yaro, za a gurfanar da shi a gaban kotu”
Daga qarshe SP ya yi kira ga al’umma
da su bi doka da qa’ida.
Malamin ya tabbatar da cewa
iyayen yaran suna biyan kuxin abincin yara naira xari da arba’in kullum ga duk
yaro xaya wanda za a saya masa abinci, malamin ya qara da cewa ginin mallakin
makarantar ne kuma za ta kai shekara goma da ginawa. Saidai ba a tabbatar da
cewa malamai nawa ne ke gudanar da makarantar ba.
An dai ga yara da yawa a cikin
xakin da aka yi wa qofar qarfe inda yaran ke leqowa, an ga kuma wani qaramin
xaki wanda ya kasance kamar falo inda ake ajiye akwatunan kayan yaran, sannan
kuma an ga kwanuka da robobi a cikin falon.
Ba wannan ba ne karo na farko da
aka fara gano makarantun da ake horar da yara ko matasa ba, kodayake malaman
sun yi iqirarin cewa iyayen yaran ne ke kawo su saboda sun kangare masu, don
haka sai ake kawo su irin wannan yara makaranta don su samu tarbiyya. Amma yanayin
azabar da ake ganawa yaran yafi qarfin jikunansu.
Wasu Labarai:
0 Comments