Talla

An Kama Mai Kaiwa Bello Turji Makamai

Daga: Muhammad Abdallah

SOKOTO, NAJERIYA - Yansanda a Jihar Sokoto sun kama wani ƙasurgumin ɓarawo dake da alaƙa da Bello Turji. An kama Musa Kamarawa ne a wani samame da rundunar da kai a yunƙurinsu na kakkaɓe ɓarayin daji. ƙasurgumin ɓarawon matashi ne ɗan shekara talatin da uku kuma yana da kusanci da shahararren ɓarayon wanda aka fi sani da sunan Bello Turji.

Ta bakin muƙadashin babban sufeton yansanda na Sokoto da Kebbi da Zamfara wato DIG Ahmed Zaki Gwandu, ya ce, dakarun rundunar Operation Sahara Storm sun kai samame a ƙananan hukumomin Raɓah da Goronyo da Ilella.

A samamen da suka kai, sun yi nasarar kama ɓarayi wannan ƙasurgumin ɓarawo, wanda ya bayyana cewa yana kai wa Bello Turji makamai da harsasai da kuma bindigogi. Ko lokacin da aka kama shi, yana shirin kai wa Bello Turji wasu makamai masu ɗinbin yawa waɗanda kuɗinsu zai kai miliyan ashirin ta takwas.

Duk a cikin ɓarayin, an kama wani shahararren ɓarawo dake yankin Dege ta Jihar Filato, ɓarawon ya daɗe yana dilancin makamai, a wannan kamun da aka yi masa ya kawo bindigu ƙirar AK47 ne a yankunan Zamfara da Sokoto da Katsina, kafin ya saida bindigar ne aka yi nasarar kama shi.

An kama ɓarayi mutum talatin da bakwai masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa da kai hare-hare da yin infomanci da yin fashi da makami, haka kuma an kama harsasai dubu ɗaya da ɗari huɗu da ƙanan bindigogi guda huɗu da kakin soja guda uku da babur huɗu da wayoyin hannu guda sha shidda da shanu guda ɗari da hamsin da layukan waya da gurneti dai sauran makamai.

ASP Sanusi Abubakar, mai Magana a yawon yansandan Jihar Sokoto ya bayyana cewa an samu nasarar kama ɓarayin ne ta hanayr aikin haɗin guiwa tsakanin sassan hukumar yansanda. Bayan waɗanda aka kama an kuma fatatti wasu ɓarayin da dama a dajin gudun-gudun da Raɓah da Isa da Bungo da Sangari da Dunawa Tsamaye da Tangaza da Heli da Goronyo da Mayel da Sakanau da Kuka da Zangon Isu da wasu ƙauyukan da dama.

 Bello Turji dai na daga cikin shahararrun ɓarayin da suke satar mutane don karɓar kuɗin fansa da kai hare-hare da saka haraji a wasu garuruwa da tursasa hakimai da magadda da masu unguwanni su biya shi hara shi. Ko baya-bayan nan saida ya saki wasu mutane da ya kama a yunƙurinsa na yin sulhu da gwamnati. An dai taɓa ganin wata wasiƙa da ake zargin shi ne ya rubuta inda ya nemi ayi masa sulhu don kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Garuruwan Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna da Nija na daga cikin Jihohin dake fama da ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu Labarai:

  1. Yaran da Aka Kashe Bayan Hanifa
  2. Jiragen Yaƙi Na Super Tucano Sun Kashe Kwamandan Iswap
  3. Wani Matashi Ya Rataye Kansa A Jigawa

Post a Comment

0 Comments