Daga: Muhammad Abdallah
KANO, NAJERIYA — A yau ne dai aka sake zama kotu don sauraron ƙarar da aka shigar wadda ake zargin Abdulmalik Tanko tare da wasu mutane huɗu da kulla tsurkun kashe Hanifa Abubakar yarinya 'yar shekara biyar wadda malaminta ya yaudara sannan ya sace ta ya kuma nemi kuɗin fansa wajen mahaifanta bayan ya kashe ta, ta hanyar sanya mata maganin kashe ɓera a cikin kwalbar lemu.
Kotun
Majistare dake sauraron ƙarar ta umurci jami’ai da su ci gaba da tsare waɗanda
ake zargi da kisan har zuwa ranar tara ga watan Fabrairu shekara ta 2022.
Lauyoyin
gwamnati ne suka nemi a sake tsare mutanen huɗu da ake zargi har zuwa wannan
rana, saboda su samu damar sake gurfanar da waɗanda ake zargi a wata babbar
kotu wadda ke da hurumin sauraron wannan ƙara da aka shigar.
Barista Aisha
Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnati, haka kuma Majistaren dake Gidan
Murtala a Birnin Kano ce ta fara sauraron ƙarar da aka shigar.
An ga hotunan
Malamin su Hanifa wanda ake zargi da kisanta, sanye da shuɗiyar riga, haka kuma
an gan shi ya saisaye kansa ba kamar yadda ya fita hayyacinsa ba a can baya
saboda tashin hankalin da ya shiga na kashe ɗalibarsa. Haka kuma an ga hoton abokinsa wanda ya taimaka masa wajen rife gawar Hanifa, an ga hotun matar da
aka kitsa sace Hanifa da farko sanye da abaya ta rufe fuskarta da takunkumin
fuska.
Bayan kashe Hanifa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar Hanifa sannan kuma ya
jinjina wa 'yansandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa
Abubakar mai shekara biyar. Kisan Hanifa dai wani abun ban tsoro ne, wanda ya
tayar da hankullan iyaye tare da ɗalibai waɗanda ke zuwa makarantu don neman
ilimi.
Haka kuma, Wani Mahaifi ya yi niyar ba mahaifan Hanifa ɗiyarsa mai
suna Fatima don rage masu raɗaɗi daga cin amanar da aka yi masu. Hanifa dai
yarinya ce ƴar shekara 5 wadda wani malaminta ya sace sannan ya yi mata kisan
gilla ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin kangayen makarantarsu.
Malam
Abdullahi Ahmed Latus mazauni ne a ƙaramsr hukumar Darazo dake Jihar Bauchi ya
faɗi cewa tuni ya fara ƙudurta bayar da ɗiyarsa da mahaifan Hanifa domin rage
masu kewar rashin ɗiyarsu.
Saidai kuma, Rundunar
'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su
Hanifa Abubakar, yarinyar nan 'yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar
da yi mata kisan gilla ta hanyar bata guba da cikin kwalbar lemu ta sha sannan
ya saka ta cikin buhu ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin harabar makarantarsu,
daga bisani kuma ya yi ta tsorata mahaifan Hanifa don su bashi kuɗin fansarta.
Bayan kashe Hanifa mutane sun ci gaba da yaɗa hotunan wasu yara da aka kashe bayan kisan Hanifa, yarinyar da wani malaminta ya sace sannan ya kashe ta hanyar sanya mata guba a cikin kwalbar lemu. An ta yaɗa hotunan wasu yaran da aka kashe kafin a kashe Hanifa.
Satar yara a garuwan Kano da Kaduna da Abuja da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare, inda ake yaudarar yaran a sace wasu ayi masu fyaɗe sannan kuma a nemi kuɗin fansa wasu kuwa kuɗin fansa ake nema sannan a kashe su. Ko kwanakin baya saida aka kama wani mutum da yake cin naman mutane a garin Gusau dake Jihar Zamfara wanda wani dake yi masa aiki ya sace wani yaro tare da kashe shi. Ga dai jerin sunane wasu yara da aka sace waɗanda ake yaɗawa a dandalin sada zumunta:
- Haidar Da Aka Sace A Unguwar Na'ibawa Dake Kano
- Aisha Sani Da Aka Sace A Tudun Wada Dake Kano
- Yaro da aka sace a Karkasara dake Kano
- An Sace Mohammed Kabiru Unguwar A Badarawa Dake Kaduna
- An Sace Husnah Garin Zariya
- Wata Uwa Da Ta Kashe Yayanta Guda Biyu A Unguwar Sagagi Dake Kano
Wasu Labarai:
0 Comments