Daga: Sheikh Malam Dr. Mohd
Kamar yadda mazaje ke da irin nasu zaɓin
dangane da irin maccen da za suyi tarayya da ita a zamantakewar aure, to haka
suma mata suna da irin nasu zaɓin dangane da irin mazajen da za su yi rayuwar
aure da su. Tamkar yadda mazaje ke buƙatar farar mace, to suma wasu matan suna
buƙatar farin namiji, wasu kuma baƙin namiji suke buƙata. Akwai matan da suke
buƙatar dogon namiji, wasu kuma sun fi son namiji gajere. Wasu matan sun fi son
namiji mai hali wato mai kuɗi, amman wasu kuma sun fi son namiji mai rufin
asiri kuma mai Ilimi.
Akwai matan da ke son namiji mai ƙiba, kuma dogo, amman wasu matan sunfi
son marar ƙiba.
Wata matar tana buƙatar ta mallaki wani
babban ma'aikacin gwwmnati, wata kuma tafi son ɗan kasuwa.
To
haka dai al'amarin yake kowace 'ya mace akwai irin nata zaɓin dangane da
mazajen da zasu aure.
Amman bisa dacewam ya 'yar uwa a lokacin da
ki ka tashi zaɓen namiji da za ki aura ya kamata kiyi la'akari da:-
- Namiji mai gaskiya da riƙon amana.
- Namiji mai tsoron Allah.
- Namiji mai ilimin addini da na zamani.
- Namiji adali.
- Namiji mai sakin fuska da yafe kura-kurai.
- Namiji mai ƙoƙarin neman halas ɗinsa.
- Namiji mai baiwa da karamci.
- Namiji mai tsafta.
- Namiji mai mutunci.
'Yar uwa idan ki kayi la'akari da waɗannan
abubuwa a lokacin zaɓen abokin zama to kuwa da yardar Allah za kiyi zaɓi na
gari.
Bayan haka 'yar uwa akwai waɗansu halaye da
ɗabi'u da ya kamata kiyi nazarinsu.
Duk namijin dake da su to ba abin so bane
waɗannan halaye da ɗabi'un sun haɗa da:-
- Mai girman kai
- Jahili
- Marowaci
- Mayaudari
- Fasiƙi
- Maƙaryaci
- Asharari
- Mai wulaƙanci
- Ƙazami
- Azzalumi
- Macuci
- Mai nisantar jama'a
- Mai yawan aikata zunubai
- Mai izgili
- Mai hassada
- Mai hana Alkhairi
- Mai katsalandan
- Marar sirri
- Makwaɗaici
- Marar cika alƙawari.
Za ku iya fadin ra'ayoyinku a wajen Komet, za mu wallafa ra'ayoyin da suka fi jan hankali.
0 Comments