Daga: Hauwa'u Bello
ABUJA, NAJERIYA - Abba Kyari ɗansa da ake wa hasashen cewa yana daga cikin masu gaskiya, wanda aka dakatar saboda tuhumar da jami’an FBI ke yi masa wanda wani hatsabibin ɗan damfara ta yanar gizo ya ce ya taba bashi wasu maƙudan kuɗi, ya musanta zargin da ake yi masa na haɗaka da wasu jami’ai na NDLE don salwantar da wata hodar iblis mai ɗinbin yawa.
Yan’uwansa
‘yansada ne suka kama Abba Kyari sannan suka miƙa shi ga jami’an NDLEA bayan
jam’ian sun neme shi ruwa jallo. Hukumar ta zarge shi da alaƙa da wata ƙungiyar
masu safarar miyagun ƙwayoyi dake aiki tsakanin Najeriya da Habasha da kuma
Barazil.
Lauyan
Abba Kyari ya shaida wa wata babbar kotu dake birnin Abuja cewa wannan zance ƙirƙirarre
ne babu ko ƙwayar zarrar gaskiya a cikinsa.
A
cikin zargin da hukumar take yi wa Abba Kyari ta ce, ya yi yunƙurin bai wa jami’anta
cin hanci don su ɓatar da kilo 25 na hodar ibilis da jami’ansa suka kama, da
farko dai ya fara neman a salwantar da kilo biyar a cikin hodar da aka kama
amma daga bisani ya nemi haɗa baki da jami’an NDLEA da su ɓatar da wasu adadi
ha kilo ɗin hodar sannan su miƙa wani adadi.
Saidai
Abba Kyari ta bakin lauyansa ya musanta duk waɗannan zarge-zarge da ake yi
masa.
Ya
ce, jami’an hukumar NDLEA ne suka masa gadar zare bayan ya nace sai an bayar da
lada ga wanda ya bayar da labarin inda aka ɓoye hodar da kuma yadda za a kama
wanda ke shigo da hodar.
Ɗaya
daga cikin lauyoyin Abba Kyari mai suna Hamza Nuhu ya tabbatar da cewa sun
gabatar da takardar neman belinsa. Ya yi zargin cewa an tsare Abba Kyari fiye
da awa 24 ba tare da gabatar da shi kotu ba kan zarginsa da ake yi, wanda hakan
ya saɓa wa doka ta yancinsa na ɗan adam.
Ana
sa ran kotu za ta saurari buƙatar lauyoyinsa a ranar alhamis.
Wasu Labarai
0 Comments