Daga: Hauwa'u Bello
05 Janairu, 2022
Za a fara haska shiri mai dogon zango a ranar laraba wanda ya yi daidai da 6 ga watan Janairu, 2022. Za a nuna shirin ne fa masu kallon fina-finan Kannywood. Shirin Gidan Badamasi zango na ɗaya da na biyu da na uku sun ja hankalin masu kallo.
Shiri ne na nishaɗi da faɗakarwa da nusar da mutane cikin ban dariya. Shahararren marubucin nan Nazir Adam Saleh ne ya rubuta labarin. Falalu Ɗoroyi ne ya shirya fim ɗin ya bada umurni ya kuma fito a matsayin tauraro a matsayin Taska. Tashar Arewa24 ke nuna shirin kuma ita ce za ta ci gaba da nunawa.
Labarin Alhaji Badamasi da ya'yansa waɗanda ya yi alƙawarin kuɗi, babban ɗansa shi ne yaya Ɗan-kwambo. Ya yi aure-aure inda ya auri mata kusan goma sha biyu. Attajiri ne amma wanda baya son fidda kuɗinsa ko kaɗan.
Dorayi, ya ce abin da ya bambanta zango na huɗu da sauran na baya shi ne an ɗauke shi ne a sassa daban-daban na Jihar Kaduna.
Ya ƙara da cewa, shi ne shiri na farko da ya fara karɓar koken masu kallo tare da aiwatar da tsakurensu a cikin fim din.
Ɗoroyi ya ce,
Gidan Badamasi zango na huɗu zai kayatar da ’yan kallo saboda ya zo da baƙon abu a cikin fina-finai masu dogon zango.
Ya ƙara da cewa,
Mun karɓi tsakure daga masu kallo wanda shi ne ya sanya shirin ya kasance na musamman.
A cikin shiri na huɗu za a ga manyan ’yan wasa da suka haɗa da Adam A. Zango, sannan za a ga Mustapha Naburaska, Suleman Bosho, Dan Kwambo, Falalu A. Dorayi, Tijjani Asase, Umma Shehu, Hadiza Kabara, Ado Gwanja.
0 Comments