Daga: Muhammad Abdallah
SOKOTO,
NAJERIYA - Wasu ɓarayi da ake kyautata
zaton yan bindiga ne na yin shigar mata don kai hare-hare a yankunan ƙananan
hukumomin Sokoto. Ɓarayin dajin su kanyi shigar mata su saka hijabi da ɗan
kwali da rigara mama sannan su shiga gari su saje cikin mutane.
Ƙananan hukumomin Sokoto kamar su
Illela na daga cikin hukumar da ta yi ta samun hare-haren ɓarayi masu satar mutane
don karɓar kuɗin fansa. Kodayake yanzu matsalar tayi sauƙi sosai inda su ɓarayin
da kansu suke ta neman sasanci. Bayan wannan kuma sai ɓarayin suka ɓullo da
wani sabon salo na yin shigar mata. A Jihar Sokoto yanzu haka ana samun koke-koken
al’umma game da yadda ɓarayin ke yin shigar mata sannan su shige cikin mutane.
Yankin Illela dake gabashin jihar,
jama’ar yankin sun koka da cewa, kusan kullum sai an samu yan bindiga sun kai
farmaki su kashe mutane ko sus ace mutane don neman kuɗin fansa.
Bello Isa Ambarura shi ne Wakilin
jama'ar yankin a majalisar dokokin jihar Sakoto, ya kuma ce 'yan bindigan sun
sace mutum bakwai da kuma matar Hakimin ƙauyen.
Shi ma hakimin kauyen Luggahuru dake
yankin Illela ya bayyana yadda abin ke addabar jama'ar sa. Kodayake yankin
Illela na iyaka da Najeriya da Nijar kuma a wannan yanki yan sa kai na bakin ƙoƙarinsu
wajen daƙile hare-haren ɓarayin daji. Duk da cewa akwai jami'an tsaro na
gwamnati a yankin amma a cewar wakilin jama'ar hakan bai hana ‘yan bindi cin Karen
su ba babbaka ba a yankin.
Mazauna yankin sun nuna damuwa a kan
yanayin da suka tsinci kansu. Wani mazaunin yankin ya ce,
"Yanzu har shigar burtu suke
yi, ko su yi shigar mata su saka hijabi, su shiga gari su labe. Kullum abin da
ke faruwa kenan."
Garuruwan Katsina da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane
don karɓar kuɗin fansa. Ko kwanan saida wasu ɓarayi suka kai hari tare da sace
wasu matafiya a Jihar Kaduna tsakanin Kaduna da Birnin Gwari kodayake Jami’an
tsaro sun kuɓutar da matafiyan.
Wasu Labarai:
0 Comments