Talla

Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano

 12 Janairu, 2022

Daga: Hauwa'u Bello

KANO, NAJERIYA - Wasu 'yan bindiga da ba a san su ba sun sace mahaifiyar Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Jihar Kano wato Isiyaku Ali Danja da tsakar daren Laraba.

Maharan sun shiga gidan mahaifiyar ɗan majalisar mai suna Hajiya Zainab da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa da misalin ƙarfe ɗaya na dare, ɓarayin na ɗauke da makamai, bayan sun shiga gidan sai suka tursasa wasu dake cikin gidan don su nuna masu ɗakin Hajiya wato mahaifiyar ɗan majalisar. 

Ɗaya daga cikin ya'yan ɗan majalisar ya ce, har yanzu ɓarayin ba su tuntuɓi kowa ba. 

Honorabul Isiyaku Ali Ɗanja, shi ne tsohon Kakakin Majalisar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.

Ba a cika samun hare-haren ɓarayi a Jihar Kano ba, amma garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da harin ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu Rahotanni

  1. Masari Ya Canza Zaɓen Ƙananan Hukumomi
  2. Sanata Aleiro Ya Buɗe Ofishin APC
  3. Najeriya ta ci Masar 1 - 0

Post a Comment

0 Comments