Daga: Muhammad Abdallah
11 Janairu,
2022
KANO,
NIJERIYA - Ƙungiyar masu Adaidaita sun janye yajin aiki a Jihar Kano, Barrista
Abba Hikima wato lauyan da ke kare ƙungiyar shi ya sanarwa da matakin da
ƙungiyar ta ɗauka na janye yajin aikin.
Tun a ranar Litinin, 10 ga watan Janairun
2022 aka wayi gari da yajin aikin direbobin Adaidaita.
Masu adaidaita
na zargin cewa ana karɓar masu kuɗi da sunan rigistar lambar motarsu wanda
wannan ne yasa suka tsunduma yajin aikin. Haka kuma ana sanya masu haraji mai
yawa inda suke biyan naira ɗari duk kullum kuma daga bisani aka maida harajin
naira ɗari da ashiri duk kullum.
Duk da kiraye-kirayen da suke yi na gwamnati
ta rage masu biyan harajin ranakun Lahadi tun da jami'an hukumar Karota ba sa
fita aiki a ranar amma kiraye-kirayen ya ci tura.
A ɗayan
hannun, gwamnatin Kano na ganin kyautatawar da take yi wa masu adaidaita, haka
kuma, basu ganin irin karamcin da ake yi masu wajen rage masu karɓar haraji.
Yajin aikin dai ya ja tsallawar ababen hawa
da taƙaitarsu a faɗin birnin Kano.
Wasu Labarai:
0 Comments