Talla

Yadda Yan Wasan Najeriya Suka Lallasa Masar da Sudan

 Daga: Hauwa'u Bello

ABUJA, NAJERIYA - Yan wasan Super Eagle da suke take leda waƙanda ke wakiltar tutar Najeriya sun lallasa ƙasar Sudan da ci ƙaya da nema sannan suka lallasa ƙasar Sudan da ci uku da ƙaya a wasannin da suka kara da ƙasashen biyu a mabambanta lokuttan a wasannin cin kofin AFCON.

A ranar Laraba ne ƙasar Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau kodayake ta riga ta shiga zagaye na gaba.

Najeriya ta samu damar shiga zagayen ‘yan sha shidda bayan da ta doke Sudan a wasanta na biyu a gasar cin kofin nahiyar da ake yi a Kamaru a a garin Garoua, Ƙasashen suna cikin Rukuni na D ne rukunin da ya haƙa ƙasashen: Najeriya da Guinea-Bissau da Sudan da Masar.

Nigeriya

1

1

0

0

3

1

 Guinea-Bissau

1

0

1

0

1

0

 Sudan

1

0

1

0

1

0

 Masar

A wasan ta yi da Masar, Kungiyar kwallon kafar Najeriya wato Super Eagles, ta zura kwallonta ta farko a ragar Masar. A cikin mintina 30 da take wasan ne ɗan wasa Kelechi Iheanacho ya zura kwallon. Kwallon da Iheanacho ya zura ya tabbatar da nasarar da kungiyar Super eagle ta samu ya yi wasan da aka gwabza. ‘Yan wasa Moses Simo da Joe Aribo da Maduka Okoye da Mohammed Salah sun taka muhimmiyar rawa, saidai kwallon da ƙan wasan Super Eagles ya jefa a ragar Masar ta kashe wa ‘yan wasan ƙasar Masar karsashi.

Haka kuma, ‘Yan wasan na Super Eagles sun sake nuna hazaƙarsu inda suka doke Sudan da ci uku da ƙaya, Samuel Chukwueze ne ya fara zura kwallon farko a minti na uku da fara wasa. Kwallo ta biyu kuma ta zo ne daga Taiwo Awoniyi gab da za a tafi hutun rabin lokaci, wato a minti na arba’in da biyar. Lokacin da aka dawo daga hutun rabin lokacin sai Moses Simon shi ma ya same jefa kwallo a raga wato a daidai minti na arba’in da shidda.

Duk da haka, daidai minti na saba’in da fara wasa sai ƙasar Sudan ta samu bugun fenariti wacce Khedr Safour Daiyeen ya buga ya kuma ci. ‘yan wasan Najeriya sun yi ƙoƙari sosai inda suka nuna hazaƙa da kishi da nuna kwarewa a wannan rukuni. Yanzu haka tana daga cikin ƙasashen da suka fi jefa kwallo a raga a rukuninsu na D.

Najeriya ta yi ƙoƙarin ganin ta mallaki gurbi a zagayen da za a fara sallamar ƙasashe zuwa gida. A ranar Laraba Najeriya za ta ƙara buga kwallo da Guinea-Bissau, ita kuwa ƙasar Sudan za ta fafata da Masar. Sau uku Najeriya tana lashe kofin na AFCON, ko a shekarar 2013 ƙasar ce ta ƙauki kofin na AFCON.

Wasu Labarai:

  1. Matasa Sune Jigon Siyasa a Kowace Tafiya
  2. Wani Mahaifi Ya yiwa Ƴarsa ƴar Shekara 3 Fyaɗe
  3. Jarumar Fina-Finai Ta Zargi Kanta Da Ƙin Sake Yin Wani Aure

 


Post a Comment

0 Comments