Daga: Muhammad Abdallah
5 Janairu, 2022
A wannan satin ne shahrarren ɗan fashin daji wato Bello Turji ya saki wasu mutane da ya yi garkuwa da su.
Bello Turji ya shahara sosai saboda rashin tausayi da kuma haraji da yake yanka wa wasu ƙauyuka dake kusa da dabarsa, tare da sauke wasu magaidai d masu riƙe da sarautar gargajiya yana ɗora yaransa.
Wani daga cikin sama da mutumen da Bello Turjin ya saka, wanda yaran Bello Turji suka sace a hanyar Kaura Namoda zuwa Sabon Birni ya ce sun sha baƙar wuya a hannun Turji.
A wata hira da ya yi a wata tasha ta Youtube, ya bayyana cewa ya shafe kwana 32 a hannun masu garkuwa da mutane, amma duk tsawon waɗannan kwanakin bai samu ganin Bello Turji.
Mutumin ya bayyana cewa ƴan bindigan sun faɗa masu abubuwa da dama, inda daga ciki suke yawan ba su labarin cewa a rayuwarsu babu abin da suke tsoro kamar jirgin soji.
Ƴan bindigar sun shaida masa cewa don jami'in tsaro ya je wurinsu a ƙasa ba za su ji tsoro ba domin suna da tabbacin cewq za su kashe su, ya kuma bayyana cewa har nema suke sojoji su zo wajen su don su yi ramuwar gayya.
Ya ce,
Da sun ga jirgin sojoji za su ɗauremu da kaca su ƙara tsuke mu su tsere su je wajen dutsi su ɓoye.
Sun ga jirgin sojijoji ya shiga daji har ya taɓa jefa masu bam.
Mutumin ya tabatar da cewa bam ɗin da jirgin yaƙin soji ya jefa a cikin daji har sai da ya ƙona makarantar Turji da kuma kayan abincinsa.
Ya bayyana cewa jirgin bai illata ko mutum ɗaya ba cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
A kwanakin baya ne Bello Turji ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla da kuma yin sulhu.
An samu wata takarda da ake zargin cewa Bello Turji ne ya rubuta ta. A cikin takardar Bello Turji ya nemi a yi sasanci.
Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments