Daga: Muhammad Abdallah
ZAMFARA, NIJERIYA — Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau shugaban wannan ƙungiyar
wadda ta shahara da kai hare-hare wato ƙungiyar Boko Haram, da Abu Musab Al-barnawi
shugaban ISWAP babu wani sunan ɗan ta’adda ta ya shahara a tsakanin mutane
kamar sunan Bello Turji, kodayake sunan ya yi shuhura ne saboda sabon salo da
ya ɓullo da shi wajen kai hare-harensa da nuna rashin tausayi da yanka wa
mutane da garuruwa haraji.
Ko shahararren malamin nan na
Sokoto wato Sheikh Bello Yabo ya sha ambatar sunansa, har ma an taɓa jin ya yi
kokwanton cewa Bello Turjin ya taɓa ɗaukar karatu a wajensa. Haka kuma shi
Bello Turjin da kansa ya taɓa ambatar sunan shahararen Malamin nan wanda yake
ta ƙoƙarin kawo sulhu tsakanin ɓarayin daji da hukumomi wato Sheikh Ahmed Gumi
a cikin takardar da ake zargin shi ya rubutawa Sarkin Musulmi da Gwamnan
Zamfara da kuma shugaban Ƙasa yana neman sulhu.
shin waye Bello Turji? Tambayar da
aka daɗe ana yi kenan tsakanin mutane, sunan da ya shahara a cikin ‘yan ta’adda.
Bello Turji yana da abokai kamar su, Alhaji Ɗan Auta, da Bacalla Ɓingyal da Ɓaleri
da Bello Kagara da Danbokolo da Malam Ila Manawa wanda ɗa ne ga Maigarin Manawa.
Dukkansu suna gudanar da sana’a
iri ɗaya, kuma suna da alaƙa ta kusa, a iya cewa ma shi Bello Turji shi ne
shugabansu, kuma dukkansu matasa ne masu arzikin shanaye da abun duniya mai
yawa.
A cikin wasiƙar da ake zargi shi
ne ya rubuta ta, ga abinda ya ce,
“…Muna godiya ga Allah (SWA) daya
nuna mana wannan lokaci, ga saƙo nan zuwa ga Masarautar Shinkafi, zuwa ga Mai
Girma Gwamnan Zamfara Barden Ƙasar Hausa, Alhaji Muhammdu Bello Matawalle
Maradun, zuwa ga Shugaban Ƙasa Maigirma General Buhari (R.T.A).
Wanda ya rubuto wannan takarda
shi ne: Muhammadu Bello Turji Kacalla…”
Bello Turji Kacalla an haife shi
a garin shinkafi, inda ya girma sannan ya fara karatun boko da Islamiyya, ya kamala
firamare sannan ya ci gaba da kasuwanci mahaifinsa ke jan shi zuwa kasuwanni
don sayen dabbobi. Mahaifinsa mai suna Usman amma an fi kiransa da sunan Mani
na Maraƙe ɗan kasuwa ne kuma mai arziƙi bawan Allah wanda baya son tashin
hankali. Sunan mahaifiyarsa ‘Yar Kagara, haka kuma yana da wani ɗan uwa mai
suna Danbokolo wanda suke aikata ta’asar tare, shi ne ma babban yaronsa.
Mahaifinsa baya son wannan ta’asar
da Bello Turji yake aikatawa wanda hakan yasa ya yi hijira ya koma garin Kura
dake cikin Jihar Kano, yanzu kuma ana tunanin ya tashi daga Kura ya koma wani
gari dake Jihar Jigawa. Dukkan dangin Bello Turji basu mu’amala da shi in bayan
wannan babban yaro nasa wato Danbokolo.
Bello Turji bai daɗe da shiga harkar
satar mutane don karɓar kuɗin fansa ba, ko lokacin da aka kashe Buharin Daji,
shi Bello Turji yana ƙarami kuma ana zuwa kasuwa dashi, shekarunsa ba za su gaza
ashirin da bakwai ba kuma ba za su wuce talatin da biyar ba.
Rashin tausayinsa da kai
hare-hare da satar shanu da sawa talakawa haraji su suka ƙara sawa ya shahara
sosai. Ko a satin daya gabata sai da wata jarida ta ruwaito cewa an kashe shi. Amma
an tabbatar da cewa bas hi ne aka kashe ba, yana na da ransa, yana kuma ci gaba
da neman sulhu wajen Gwamnati.
Garuruwan Katsina da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-hare ɓarayin daji masu satar mutane
don karɓar kuɗin fansa. Bello Turji na ɗaya daga cikin ɓarayin da yake da yara
masu tarin yawa.
0 Comments