Talla

Wata Mata ta Kashe kanta a Kano

 Daga: Aminu Abdullahi

KANO, NAJERIYA - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata da ake zargin ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

'Yan sandan dai sun ce matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga, inda ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo.

A cewar ɗan uwan marigayiyar mai suna Muhammad Sanusi, kafin ‘yar uwar tasu ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato kankare, wanda har sai da ta kai ga sun rufe ta a ɗaki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai taɓin hankali.

Ya ƙara da cewa a ranar da suka buɗe ta ne ta fasa gilashin tagar ɗakin da aka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro.

A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Kano da ke arewacin Najeriya, wanda wasu daga cikinsu aka alaƙanta da matsalar ƙwaƙwalwa.

Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa.

Wasu Labarai:

  1. An Sace Wani Basarake A Palato
  2. Ɓarayin Daji Sun Kai Sabbin Hare-hare
  3. Mutum da Muhallinsa

Post a Comment

0 Comments